Ba bu hannun mu cikin 'dambarwar taron Kwankwaso a garin Abuja - APC

Ba bu hannun mu cikin 'dambarwar taron Kwankwaso a garin Abuja - APC

Biyo bayan dambarwar haramtawa Kwankwaso gudanar da taron kaddamar da aniyyarsa ta takarar kujerar shugaban kasa a farfajiyar taro ta Eagles Square, jam'iyyar APC ta musanta zargi tare da bayyana cewa ko kadan ba bu hannunta cikin wannan lamari.

Ko shakka babu an haramtawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, amfani da dandalin Eagle Square wajen gudanar da taron bayyana kudirin sa na takarar kujerar shugaban kasa a ranar Larabar da ta gabata.

Kamar yadda wani jigo na kwamitin yakin neman zabe na Kwankwaso, Kwamared Aminu Abdussalam, ya shaidawa manema labarai an BBC cewa an hana su gudanar da wannan taro bayan tuni sun riga da biyan kudi na hayar farfajiyar.

A sanadiyar haka dole kanwar naki ta sanya Sanata Kwankwaso ya gudanar da taron kaddamar da kudirin sa a wani babban Otel na Achida a ranar Larabar da ta gabata.

Ba bu hannun mu cikin 'dambarwar taron Kwankwaso a garin Abuja - APC
Ba bu hannun mu cikin 'dambarwar taron Kwankwaso a garin Abuja - APC
Asali: Twitter

A yayin musanta zargi dangane da hannun jam'iyyar APC cikin wannan dambarwa ta haramtawa Kwankwaso amfani da farfajiyar Eagles Square wajen gudanar da taron sa, ta bayyana cewa ko kadan ba ta da hannu cikin wannan lamari.

KARANTA KUMA: 2019: Za a gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci - Shugaba Buhari ya sha alwashi ga Firai Ministar Birtaniya, Theresa May

Jam'iyyar a yayin ci gaba da wanke kanta ta kuma bayyana cewa, wannan takkadama tsakanin Kwankwaso ne da kuma kamfanin mai zaman kansa dake kula da filin na Eagles Square da ya hana gudanar da taron.

Kamar yadda shafin jaridar Sahara Reporters ya ruwaito, jam'iyyar ta wanke hannunta kan wannan zargi cikin wani sako da ta bayyana a shafinta na sada zumunta, tare da jan gora na cewar nasara a zaben 2019 ta na ga yawan kuri'u ta masu hangen nesa ta tantance wanda ke da akida ta ci gaban kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel