Na ji dadin zuwana Najeriya – Theresa May

Na ji dadin zuwana Najeriya – Theresa May

- Firam Minista Birtaniya ta garzaya jihar Legas bayan ganawa da shugaba Buhari

- Sun tattauna kan muhimmanci kasuwanci tsakanin Najeriya da Birtaniya

Firam minstan kasar Birtaniya, Theresa May, ta bayyana cewa ta ji dadin zuwanta Najeriya kuma tana kyautata zaton karuwan kasuwanci da hannun jari tsakanin Najeriya da kasar Birtaniya.

Ta laburta hakan ne ga manema labarai yayinda ya dira a babban filin jirgin saman Mutala Muhammed da ke Ikeja jihar Legas. Daga nan sai ta fita daga kasar misalin karfe 8:10 na dare.

Tace: “Na je Abuja kuma gani a Legas domin ganin yadda kasuwanci ke gudana a nan.”

“Muna son ganin cigaba kasuwanci da hannun jari tsakanin Najeriya da Birtaniya. Karuwan hannun jari da zai samar da ayyuka a Najeriya da Ingila. Wannan alkhairi ne ga kasashen biyu kuma na ji dadin zuwana Najeriya, ina matukar farin ciki,” .

KU KARANTA: Abinda ya sa Obasanjo ke son in zama shugaban kasa - Lamido

Gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode na jihar Legas wanda ya karbi bakuncinta daga filin jirgin saman ya ce ta kawo ziyara mai matukar muhimmanci ne kan bunkasa hannun jari a jihar da kuma kasa ga baki daya.

A cewarsa: “Ta je Abuja da farko. Abu mai muhimmanci da muka tattauna shine yadda za’a turawa za su bunkasa hannun jari a jihar Legas.”

Mun gano cewa Legas ce babbar birnin kasuwanci a Najeriya kuma dukkan hannun jari kasar Birtaniya na zaune a jihar Legas,”.

Gwamnan ya laburta cewa sun tattauna akan abinda jihar Legas keyi domin domin jawo hankulan masu sanya hannun jari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel