Kananan hukumomi 8 sun gamu ambaliyar ruwa a Kano

Kananan hukumomi 8 sun gamu ambaliyar ruwa a Kano

- Ruwa da kamar da bakin kwarya yayi gyara a wasu garuruwa na Kano

- Gwamnatin jihar tuni ta aike da jami'an agaji don kai tallafi

- Sai dai har kawo yanzu ba'a kai ga tantance yawan asarar da aka yi ba

Hukumar bayar da Agajin gaggawa tare da rage radadi ta jihar Kano ta tura jami'anta zuwa kananan hukumomi takwas da suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a fadin jihar, domin tantance irin adadin barnar da aka samu.

Kananan hukumomi 8 sun gamu ambaliyar ruwa a Kano
Kananan hukumomi 8 sun gamu ambaliyar ruwa a Kano
Asali: Facebook

Babban Sakataren hukumar Alhaji Ali Bashir ne ya bayyanawa kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) lokacin da ya ke zantawa da su a yau Alhamis.

Ya ce kawo yanzu jami'an sun ziyarci kananan hukumomi guda bakwai, wadanda suka hadar da Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Gwarzo, Dambatta da karamar hukumar Kabo da Gezawa da kuma Gabasawa.

KU KARANTA: 2019: Sheriff bai da muradin tsayawa takarar kowani kujera – Kungiya

“Kawo yanzu mun tantance irin asarar da aka yi a wadannan kananan hukumomin da muka ambata. Yanzu karamar hukumar Gabasawa ce kawai ta rage mana wajen tantance irin asarar da aka samu a karamar hukumar." Alhaji Ali ya bayyana.

Amma sai dai sakataren bai ambata adadin mutanen da iftila’in ya shafa baba, domin kuwa ya ce suna tsaka ne da tattara rahoton ambaliyar ruwan, da zarar sun kammala za su yi cikakken bayanin adadin mutanen da annobar ta shafa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel