CBN ta ci tarar bankuna 4 N5.8bn, ta umurci masu aro da MTN da su dawo da $8.1bn

CBN ta ci tarar bankuna 4 N5.8bn, ta umurci masu aro da MTN da su dawo da $8.1bn

- Bankin CBN ta ci takarar asu bankuna hudu makudan kudade

- Ta umurci kamfanin sadarwa ta MTN da ta dawo da kudaden da aka ara mata

- Bankunan da aka ci tara sune Standard Chartered Bank, Stanbic-IBTC, Citibank da kuma Diamond Bank

Babban bankin Najeriya (CBN) ta ci tarar wasu bankuna hudu makudan kudade har naira biliyan 5.87 a karkashin duba ayyukan bankula kan bauar da aron kudi ta haramtaciyyar hanya.

Ta kuma umurci hukumomin bankunan da kamfanin sadarwa ta Najeriya wato MTN da suyi gaggawar dawowa da babban bankin $8,134,312,397.63, wadda aka ararwa da kamfanin ba bisa ka’ida ba.

A jawabin da CBN ta saki a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta ta bukaci bankunan da MTN das u dawo da kudi kan abunda ta bayyana a matsayin sabama doka da ka’idojin gwamnatin tarayyar Najeriya, harma da dokar chanjin kudin waje.

CBN ta ci tarar bankuna 4 N5.8bn, ta umurci masu aro da MTN da su dawo da $8.1bn
CBN ta ci tarar bankuna 4 N5.8bn, ta umurci masu aro da MTN da su dawo da $8.1bn
Asali: Depositphotos

Bankuna hudu da aka sanyawa wannan takunkumin sun hada da Standard Chartered Bank, Stanbic-IBTC, Citibank da kuma Diamond Bank.

An tattaro cewa bankin Standard Chartered Bank ce aka ci tara mafi girma naira biliyan 2.47, yayinda aka ci tarar Stanbic IBTC naira biliyan 1.885.

KU KARANTA KUMA: An kama wata mahaukaciyar bogi da jikin ‘Dan Adam a Legas

Ita kuma Citibank Nigeria an ci tararta naira biliyan 1.265, inda ita kuma Diamond Bank aka umurceta da ta biya naira miliyan 250 saboda saba tsarin doka.

Kakakin babban bankin kasar ya kuma bayyana cewa hukuncin da aka yankewa bankunan ya biyo bayan bincike da akayi akan zarge-zargen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel