Wasu giwaye uku sun kai hari wani kauye a jihar Kebbi

Wasu giwaye uku sun kai hari wani kauye a jihar Kebbi

Wasu Giwaye guda uku da ake zargin sun kubuto daga wani dajin daban sun kai farmaki garin Zaria Kala-kala dake karamar hukumar Koko Besse a jihar Kebbi.

Mazauna garin Zaria Kala-kala sun bayyana cewar suna zargin giwayen sun kai farmaki kauyen ne bayan rasa ragowar 'yan uwansu da suka taho tare daga dajin Jamhuriyar Nijar ko dajin kasar Benin. Kazalika sun bayyana cewar suna zargin giwayen sun samu shiga yankin jihar ta Kebbi ne ta gefen tekun Chadi.

Mazauna garin sun ce ba don zuwan jami'an tsaro da wasu shugabannin al'umma ba da jama'a sun kashe daya daga cikin giwayen da aka ritsa.

Wasu giwaye uku sun kai hari wani kauye a jihar Kebbi
Wasu giwaye uku sun kai hari wani kauye a jihar Kebbi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu tayi fatali da bukatar dakatar da tsige Saraki

Kwamishinan muhalli a Kebbi, Alhaji Musa Kalgo, ya ce giwayen sun shigo jihar ne ta karamar hukumar Bagudu tare da sanar da cewar tuni suka sanar da hukumomi domin ganin wani bai samu dabbobin ba.

Kwamishinan ya kara da cewar giwayen sun tsallako ne daga kasar Benin, kuma suna da yakinin cewar hukumomin kasar zasu biyo su.

Kazalika shugaban karamar hukumar Koko Besse, Alhaji Musa Shehu, ya sanar da wakilin jaridar Daily Trust cewar gwaman jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya aiko da sakon cewar a tabbatar da cewar wani abu bai samu giwayen ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel