Kwankwasiyya: Mutane kusan 10, 000 sun kona jar hula a Jihar Kano

Kwankwasiyya: Mutane kusan 10, 000 sun kona jar hula a Jihar Kano

Labari ya zo mana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gamu da babban cikas a Kano yayin da yake kaddamar da shirin sa na neman takarar Shugaban kasa a Abuja.

Kwankwasiyya: Mutane kusan 10, 000 sun kona jar hula a Jihar Kano
Direbobin keke napep da dama a Kano sun barranta daga Kwankwaso
Asali: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa kusan mutane 10, 000 sun kona jar hula inda su ke nuna cewa sun bar Kwankwasiyya a Jihar Kano. Dubban masu harkar tukin keke-napep a Kano sun fice daga Jam’iyyar PDP sun koma APC.

Hakan na zuwa ne a ranar da kaddamar da shirin sa na fitowa takarar Shugaban kasa na zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP a cikin Garin Abuja. Direbobin na Keke-napep sun ce su na tare da Ganduje da Shugaba Buhari.

KU KARANTA: Kwankwaso yayi alkawarin gyara harkar ilmi a Najeriya

An yi bikin karbar wadanda su ka bar PDP ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata. Sani Sharu Dala wanda shi ne Jagoran wadanda su ka bar PDP ya bayyana cewa yanzu sun gano wanene tsohon Gwamna Kwankwaso.

Shugaban Jam’iyyar APC Alhaji Abdullahi Abbas yace mutanen sun kona jajayen huluna ne domin nunawa Duniya ba su tare da Kwankwaso. Gwamnatin Abdullahi Ganduje dai tayi alkawarin tafiya da kowa a Jihar ta Kano.

Dazu kun ji cewa Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya soki Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya nemi jama’a su goyi bayan duk wanda Jam’iyyar PDP ta tsaida a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel