An gano wata tsohuwa da ta ga dukkan yakin duniya biyu da aka yi (hotuna)
- Ana kyautata zaton wata mace 'yar kasar Bolivia, Julia Flores Colque ce mace mafi tsufa a duniya, shekarunta 118
- Katin shedar 'yar kasar na Colque ya nuna cewa an haife ta a watan Octoban shekarar 1900 a sansanin masu hakar ma'adinai
- A rayurta, Bolivia ta ga yakokin duniya biyu da sauye-sauyen mulki da dama
Rahotan da muka samu ya ce wata mace 'yar kasar Bolivia, Julia Flores Colque, mai shekaru 118 ce tafi kowa tsufa a duniya. Katin shedar kasa na Flora ya bayyana cewa an haife ta ne a ranar 26 ga watan Octoba shekarar 1900, hakan na nuna cewa ta ga yakokin duniya biyu da rayuwanta.
A wata hira da akayi Colque, dattijiyar ta ce tana kaunar cake da rera wakokin gargajiya kuma tana son wasa da kajin ta. Kazalika, tana da mage da kuma wani abin kida mai kama da garayya wanda ake kira charango a kauyensu na Sacaba.

Asali: Depositphotos
Ta ce an haife ta lokacin da adadin mutanen da ke kauyen bai wuce 3,000 ba amma yanzu mutane garin sun tasanma 30,000.
DUBA WANNAN: Magoya bayan Kwankwaso sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja
Duk da cewa sunanta bai shiga littafin tarihin duniya na Guinness ba, Colque ta ce hakan bai damun ta domin tana jin dadin gudanar da rayurta yadda take so.

Asali: Depositphotos
Duk da shekarunta, Colque tana karbar baki a gidanta inda take zaune da 'yar kanwarta mai shekaru 65 mai suna Agustina Berna.

Asali: Depositphotos

Asali: Depositphotos
Wani abin mamaki shine Colque bata taba aure ba a rayurta kuma bata da yara. Sai dai duk da haka tana jin dadin rayuwarta kuma tana kula da kanta ta hanyar sana'ar siyar da kayan marmari.

Asali: Depositphotos
Ba'a bayar da katin shedan haihuwa lokacin da aka haife ta sai dai Fastocin cocin katolika suna bawa mutum kadin shaida ranar da akayi masa batisma kuma gwamnatin kasar ta tantance sahihancin katin shedar na ta.

Asali: Depositphotos
Asali: Legit.ng