Gwamnatin Tarayya tana neman taimakon Bankin Duniya da Bill Gates kan Hukumar NHIS

Gwamnatin Tarayya tana neman taimakon Bankin Duniya da Bill Gates kan Hukumar NHIS

A yayin da gwamnatin tarayya ta kai makura wajen gazawa kan ci gaba daukar nauyin hukumar inshorar lafiya ta kasa watau NHIS, ta bukaci tallafi da neman agajin bankin duniya da kuma gidauniyar nan ta Bill and Melinda Foundation.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shine ya mika wannan koko na barar tallafi yayin zaman sauraron ra'ayin al'ummar Najeriya a birnin Minneapolis na kasar Amurka da aka gudanar a wannan mako.

Osinbajo ya nemi tallafin bankin na duniya tare da gidauniyar Bill and Melinda Foundation mallakin attajirin nan, Bill Gates, domin wadata al'ummar Najeriya gami da kawo sauki cikin lamuran insorar lafiyar su.

Legit.ng kamar yadda mataimakin shugaban kasar ya bayyana ta fahimci cewa, kasafin kudin kasar nan da na jihohi na bangaren lafiya ba zai wadata al'ummar baki daya ba wajen tanadi a gare su na inshorar lafiya.

Gwamnatin Tarayya tana neman taimakon Bankin Duniya da Bill Gates kan Hukumar NHIS
Gwamnatin Tarayya tana neman taimakon Bankin Duniya da Bill Gates kan Hukumar NHIS
Asali: Depositphotos

A sanadiyar haka ne gwamnatin tarayya take ci gaba da kai komo a bankin duniya da kuma gidauniyar ta Bill and Melinda domin kawo agaji na mamaye dukkanin al'ummar kasar nan ta bangaren lafiyar su da adadin su ya haura Miliyan 180.

KARANTA KUMA: Rashin adalci da nuna son kai na jam'iyyar APC ya sanya na sauya sheka zuwa PDP - Ayorinde

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai kimanin mutane miliyan bakwai cikin miliyan 180 na kasar nan dake da inshorar lafiya karkashin hukumar NHIS inda mafi akasarinsu ma'aikata ne na gwamnatin tarayya.

Kazalika gwamnatin tarayya na ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar gwamnatocin jihohi domin kawo wannan shiri na inshorar lafiya ga al'ummomin su a matsayin wani ɓangare na rage nauyin da ya rataya a wuyan hukumar NHIS ta kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel