Lalata da kananan yara: An bukaci Paparoma yayi murabus

Lalata da kananan yara: An bukaci Paparoma yayi murabus

Ana hurawa Paparoma Francis wuta kan yayi murabus daga kujerarsa sakamakon rahoton kotu a Pennsylvania da ta bayyana cewa da yiwuwan Rabaren kimanin 300 sunyi lalata da yara akalla 1000 a cocina 6.

Bayan ga haka, Rabarorin da wasu Bishop-bishop sunyi kokarin karyata labarin da kuma boye laifukan da sukeyi. Alkalin kotun Pennsylvania, Josh Shapiro, ya bayyana cewa wanna abu har a fadar Paparoma anyi kokarin boyewa.

Wannan rahoto na barazana da kujeran Paparoma Francis shekaru shida bayan ya gaji kujeran daga hannun Paparoma Benedict.

KU KARANTA: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau

Bayan labarin ya yadu a ko ina, fadar Paparoma ‘Vatican’ ta saki jawabin da ke nuna cewa cocin ta yiwa wannan babban laifi rikon sakeni kasha.

Abinda kawai kakakin cocin Paparoma, Greg Bruke, yace shine wannan abu da kotu ta bayyana yaudara ne da cuta ga wadanda abun ya faru da su.

Lalata da kananan yara: An buka Paparoma yayi murabus
Lalata da kananan yara: An buka Paparoma yayi murabus
Asali: Depositphotos

Wata kungiyar mulhidai a kasar Amurka FFRF, na kashe makudan kudi domin yayata wannan abu da kuma kira ga mutane da su fita da addinin Kirista.

Sukace: “Malama addini na lalata da kananan yara maza da mata, kuma shugabannin cocin basuyi komai akan haka ba, innama boyewa sukayi,”

“Babu Bishop din da aka kama. Shi kuma Paparoma babu abinda yake yi, sai da ya cewa mutane ‘suyi addu’a da azumi’ “

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel