Ba sani ba sabo: Wani shugaban yan sanda na fuskantar tuhuma akan cin hanci da rashawa

Ba sani ba sabo: Wani shugaban yan sanda na fuskantar tuhuma akan cin hanci da rashawa

- An fara gudanar da bincike kan wani shugaban yan sanda na Pen Cinema dake garin Yaba, da ake zargi da cin hanci da rashawa

- Al’umar wani layi dake a yankin ne suka shigar da kara kan cewar shugaban yan sanda ya karbi kudin beli har N30,000 daga wajensu

- Sai dai shugaban yan sandan wanda tuni aka dakatar dashi, ya ce sam bai aikata wannan laifi ba

Sashen binciken wadanda ake zargi da laifukan ta’addanci CIID, da ke Yaba, ya fara bincike kan wani Shugaban yan sanda a ofishin lardin rundunar na Pen Cinema, Harrison Nwabuisi, wanda aka dakatar da shi bisa zargin cin hanci da rashawa.

Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da shugaban yan sandan tare da wasu jami’an ‘yan sanda, a gaban al’umar da ke zaune a layin Alimi Ogunyemi, Ijaiye wadanda sukayi ikirarin cewa jami’an sun kwace masu kudade da sunan kudin belin mutanen da suka kama ba tare da aikata laifin komai ba.

Sai dai kamar yadda rahoton ya bayyana, Nwabuisi ya ce sam bai karbi kudin belin kowa ba, akasin ikirarin da mazauna layin suka yi na cewar shine ya tilastasu baiwa wani sajen kudin belin, wanda shi kuma ya bashi daga baya.

Wakilin jaridar Punch da ke yankin, ya tattara rahoto cewa Nwabuisi, wanda ke da matakin Sifiritanda a aikin yan sanda, ya jagoranci rundunar sa zuwa layin a ranar larabar makon da ta gabata, inda suka cafke wasu daga cikin mazauna layin.

Bayan gurfanar dashi: Shugaban yan sanda ya musanya zargin da ake masa na cin hanci da rashawa
Bayan gurfanar dashi: Shugaban yan sanda ya musanya zargin da ake masa na cin hanci da rashawa
Asali: Getty Images

KARANTA WANNAN: 2019: Ma'aikatan jihar Nasarawa sun tsaida Agara takarar gwamnan jihar

Akalla rundunar ta kamo mutane 37, inda ta garkame su a dakin ajiye masu laifi na ofishin, tare da bukatar N15,000 kudin belin kowane mutum daya.

An yi zargin cewa shugaban yan sandan, tare da hadin kan wani sajen, da aka bayyana sunansa da Bigi, sun karbi N30,000 daga hannun mutane uku a matsayin kudin belinsu.

Bayan da kwamishinan yan sanda na jihar Edgal Imohimi ya samu wannan rahoto, ya dakatar da shugaban yan sanda na lardin, tare da kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan wannan zargi.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya faru a gaban idanunsu, Ibrahim Aranjure, ya ce ya samu kiran rundunar don bada shaidar abinda ya faru, inda a ranar litinin suka je ofishin hukumar tare da wasu mutane uku da lamarin ya afku a gabansu.

Ibrahim wanda dan uwansa Sheriff na daga cikin mutanen da aka cafke, ya ce ya biya N30,000 don sallamo mutane uku.

A yayin da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, CSP Chike Oti, yake cewa ana ci gaba da bincike, shi kuma korarren shugaban yan sanda na Pen Cinema, Harrison Nwabuisi, ya ce sam bai aikata wannan laifi da ake zargin da shi ba

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel