Ba kanta: Gwamnati ta bankado kamfanin sarrafa shinkafa mai guba a Najeriya

Ba kanta: Gwamnati ta bankado kamfanin sarrafa shinkafa mai guba a Najeriya

- An bankado shinkafa mai guba a Najeriya

- An rufe kamfanin da ke sarrafa ta

- Jama'a sun cinjinawa gwamnati kan hakan

Gwamnatin jihar Ebonyi dake a shiyyar kudu maso gabashin kasar nan ta bayar da umurnin kulle fitaccen kamfanin sarrafa shinkafar nan na garin Abakalki sakamakon gano guba da kuma al-gushu a cikin shinkafar su.

Haka zalika gwamnatin ta kuma bayyana cewa tuni ta sa ayi mata bincike kan lamarin don gano musabbabin faruwar hakan tare da hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a ciki.

Ba kanta: Gwamnati ta bankado kamfanin sarrafa shinkafa mai guba a Najeriya
Ba kanta: Gwamnati ta bankado kamfanin sarrafa shinkafa mai guba a Najeriya
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tsagerun Neja Delta sun sha alwashin dagulawa Buhari lissafi

Legit.ng ta samu cewa wannan matakin na gwamnatin jihar ya fito ne daga ofishin kwamishinan yada labarai da gyaran dabi'u na jihar Sanata Emmanuel Onwe.

Jama'ar garin dai sun yi ta nuna jin dadin su game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka game da hakan tare kuma da godewa mahukuntan jihar.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta shirya tsaf domin kara gina wasu matatun mai na musamman har guda biyu a jahohin Imo da Delta dukkan su dake a kudancin Najeriya.

Kamar yadda muka samu, kamfanin albarkatun man fetur na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) shi ne ya sanar da hakan inda kuma ya kara da cewa matatun man za su rika tace akalla gangar danyen mai dubu 200 a kullum idan aka kammala su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel