Katin zabe: Gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da hutun gamagari a ranar Juma’a

Katin zabe: Gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da hutun gamagari a ranar Juma’a

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da ranar Juma’a, 1 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu don baiwa al’ummar jihar damar samun katin zabe, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito haka zalika gwamnatin jihar ta rage awanni aiki daga karfe hudu na yamma zuwa karfe biyu na rana, hakan zai fara aiki ne tun daga Talata har zuwa Alhamis.

KU KARANTA: Gwamnati ta hana Kwankwaso dandalin daya shirya kaddamar da takararsa a ciki

Mataimakin gwamnan jahar, Ibrahim Wakkala ne ya sanar da haka a ranar Talata, 28 ga watan Agusta a garin Gusau, a yayin taron masu ruwa da tsaki a al’amuran zabe game da batutuwan da suka shafi kammala aikin rajista.

Mataimakin gwamna Wakkala yace gwamnati ta yanke wannan shawara ne don baiwa wadanda basu samu damar yin rajistan katin zaben ba da su yi kafin a kammala aikin a ranar Asabar 1 ga watan Satumba.

“A matsayinmu na yan kasa nagari, ya zama wajibi mu yi rajista katin zabe, domin hakan ne kadai zai bamu damar kada kuri’unmu ga shuwagabannin da muke so a zaben 2019.” Inji wakkala.

Idan za’a tuna kusan kwanaki goma da suka gabata ne dai hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ya kamata ta rufe yin rajistan katin zaben, toh amma sai ta amsa kiranye kiranyen da jama’a suka yi mata suna bukatar a daga ranar rufewar, hakan ne yasa INEC ta kara wa’adin sati biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel