Majalisar dinkin duniya ta bayyana abinda ke rura wutar rikicin Boko Haram

Majalisar dinkin duniya ta bayyana abinda ke rura wutar rikicin Boko Haram

- Amina Muhammad, mataimakiyar babban sakataren Majali Majalisar Dinkin Duniya (MDD), ta alakanta bushewar tafkin tekun Chadi da kara rura wutar rikicin Boko Haram

- Ta bayyana cewar rashin wadataccen ruwa da kuma dusashewar albarkatun ruwa na haddasa rigingimu a kasashe da dama

- A cewar ta, kasha 40% na mutanen Duniya na fama da matsalar karancin ruwa

Babbar mataimakiyar shugaban Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Amina Mohammed, ta alakanta rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya da bushewar da tafkin tekun Chadi ke yi.

Amina ta bayyana cewar tekun na Chadi na samar da abun yi ga miliyoyin mutane dake zaune gefensa amma yanzu hakan ta canja saboda bushewar da rowan tekun ke yi.

Mataimakiyar babban sakataren na wadannan kalamai ne a birnin Stockholm na kasar Sweden yayin kaddamar da wani taro na mako guda a kan alakar ruwa da cigaban al’umma.

Majalisar dinkin duniya ta bayyana abinda ke rura wutar rikicin Boko Haram
Majalisar dinkin duniya ta bayyana abinda ke rura wutar rikicin Boko Haram
Asali: UGC

Amina ta ce ta ga yadda ta gani da idonta yadda dusashewar albarkatun cikin ruwa da rashin bawa inganta tafkuna muhimmanci ke haddasa rigingimu da barkewar aiyukan ta’addanci a kasashe da dama.

A cewar ta, ”na girma a yankin arewa maso gabas ne, yankin da samun ruwa mai tsafta da mutane zasu yi amfani da shi ba kankanin tashin hankali bane.

DUBA WANNAN: Buhari ya karbi bakuncin babban sarkin Yarabawa da masu saka hannun jari (Hotuna)

A baya tekun Chadi ne ke rike da miliyoyin mutane a yankin arewa maso gabas ta fuskar samar da aikin dogaro da kai. A yau, fiye da kasha 90% na tafkin tekun Chadi ya kwaranye. Wasu ma sun yi hasashen cewar tekun zai kafe bakidaya zuwa karshen wannan karnin da muke ciki.”

Amina ta bayyana cewar kafewar da tekun ke yi ne ta saka mutanen yankin rasa sana’o’i da kuma mutuwar kasuwanci, yanayin da ya saka ‘yan ta’adda samun wadanda zasu ja hankalinsu cikin sauki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel