Wani mahaukaci da yayi basaja don yin garkuwa da mutane ya ci dan banzan duka

Wani mahaukaci da yayi basaja don yin garkuwa da mutane ya ci dan banzan duka

Wani matashi ya ci dan banzan duka a garin Akure na jihar Ondo bayan an kama shi yana badda kama a matsayin mahaukaci, alhali yana kai ma barayin mutane bayanai game da mutanen da zasu sata ne, iniji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Litinin aka kama wannan mahaukaci dauke da wayoyin salula guda biyu a cikin rukunin gidajen Orita Obele dake garin Akure, nan da nan jama’a suka taru, suka jibgeshi iya son ransu, amma fa bai mutu ba.

KU KARANTA: Wuta ta cinye kananan yara 2 yan gida daya a wata mummunar gobara a Delta

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewa sun mika mahaukacin ga yan banga bayan ya ci na jaki a hannunsu, shaidan yayi karin bayani kamar haka: “Yace mana daga jihar Edo ya taho Ondo neman mutanen da zasu sata.

“Wasu tan kasa na gari ne suka kama shi bayan sun kwashe tsawon makonni biyu sun dakonsa tare da bin diddiginsa tun bayan da suka fahimci kamar yana daya daga cikin masu garkuwa da mutane.” Inji shi.

Sai dai shaidan gani da idon yace duk dukan da suka yi masa don jin da suwa da suwa suke aikin satar mutane, mahaukacin bai fada musu ba, don haka suke fatan Yansandan zasu binciko wannan bayani ba tare da bata lokaci ba.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jihar Ondo, Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace hukumar Yansanda zata yi duk mai yiwuwa don gudanar da aikinta yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng