Operation dirar mikiya: An yi rugu-rugu da yan baranda a Bayan Ruwa da dajin Rugu a jihar Zamfara

Operation dirar mikiya: An yi rugu-rugu da yan baranda a Bayan Ruwa da dajin Rugu a jihar Zamfara

Hukumar sojin saman Najeriya ta bayyana yadda jami’anta suka ragargaji yan baranda a kauyen Bayan Ruwa da Dajin Rugu a jihar Zamfara, Arewa maso yammacin Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani jawabi da suka saki yau Talata, 28 ga watan Agusta, 2018 ta shafin ra’ayi da sada zumuntarta.

Ga cikakken jawabin: “A cigaba da kokarin share yan baranda daga yankin Arewa maso yammacin Najeriya, hkumar sojin saman Najeriya na rundunar Operation DIRAN MIKIYA tsakanin rana 25 da 27 ga watan Agusta 2018, ta kai farmaki ga yan baranda a Bayan Ruwa da Dajin Rugu a gabashin jihar Zamfara.

An kai harin Bayan Ruwa ne sakamakon arangama da yan bindigan da wasu jami’an kasa suka yi a ranan 25 ga watan Agusta 2018. Sai jami’an suka bukaci taimakon dakarun sama. An tura jirgin yaki da mai saukar angulu wajen. Wannan gamayya ya taimaka wajen ragargazan yan barandan."

KU KARANTA: Kasar China na duba yiyuwar soke dokar kayyade haihuwa

"A ranan 26 ga watan Agusta 2018, wani jirgi mai saukar angulu yayi arangama da wani sabon waje da yan barandan suka boye bayan tsira daga harin farko. Jirgin ta musu ruwan wuta. Wasu daga cikinsu dake kokarin arcewa sun gamu sauran jami’a da suka wasu harin.

Hakazalika, hare-haren da aka kai ranan 26 da 27 ga watan Agusta 208, ya nuna cewa akwai wasu yan baranda da ke zaune a HAYIN AJHAJI da kuma gidaje a Dajin Rugu.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel