2019: APC zata yi nasara a kudu maso gabas – Hadimar Buhari

2019: APC zata yi nasara a kudu maso gabas – Hadimar Buhari

- Hadimar Shugaba Buhari tace jam’iyyar APC ce zata lashe mafi yawancin kuri’u daga yankin Kudu maso gabas a 2019

- Misis Juliet Ibekaku-Nwagwu ta bayyana cewa ta samu karfin gwiwar fadin hakan ne duba ga irin tarin kokari da gwamnatin APC tayi wajen farfado da ayyukan ci gaba da aka yasar a yankin

- Ta ce hanya daya da mutanen yankin zasu saka ma Shugaban kasar shine bashi kuri'unsu

Hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Misis Juliet Ibekaku-Nwagwu tace jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce zata lashe mafi yawancin kuri’u daga yankin Kudu maso gabas a 2019.

Ibekaku-Nwagwu ta bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai a ranar Talata, 28 ga watan Agusta a Enugu.

Ta bayyana cewa ta samu karfin gwiwar fadin hakan ne duba ga irin tarin kokari da gwamnatin APC tayi wajen farfado da ayyukan ci gaba da aka yasar a yankin arewa maso gabas.

2019: APC zata yi nasara a kudu maso gabas – Hadimar Buhari
2019: APC zata yi nasara a kudu maso gabas – Hadimar Buhari
Asali: Twitter

Hadimar shugaban kasar ta bayyana cewa yanki bata taba amfana kamar na yanzu ba tun bayan da aka dawo da mulkin damokradiyya a 1999.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya caccaki Trump kan furucin da yayi game da Buhari

Ta bayyana cewa ta hanya daya yankin zata sakawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da APC da wannan aikin alkhairi da suka yi mata shine ta hanyar basu kuri’unsu.

Ta kara da cewa Shugaba Buhari ya kunyata masu yi masa bita da kulli kuma hakan ya nuna cewa ba’a mayar da kabilar Igbo saniyar ware ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin ayyukan ginin tituna da gadoji da ta ce tana yi a kudu maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ministan watsa labarai Segun Adeyemi ya fitar ranar Litinin ta ce ya zuwa yanzu tana gudanar da ayyukan tituna da gadoji 69 a yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel