2019: Tsohon gwamnan Plateau, Jonah Jang zai bayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa a yau

2019: Tsohon gwamnan Plateau, Jonah Jang zai bayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa a yau

- Jonah Jang zai bayyana kudirinsan na son takarar kujerar shugaban kasa a yau

- Sanatan zai jagoranci mabiyansa zuwa sakatariyar jam’iyyar PDP dake garin Jos domin sanar dasu kudirinsa

- Akalla yan siyasa 15 ke neman takarar shugabancin kasa a jam'iyyar

Tsohon gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang zai bayyana kudirinsan na son takarar kujerar shugaban kasa a yau Talata, 28 ga watan Agusta a garin Jos.

Sanata Jang mai wakiltan yankin Plateau na Arewa a majalisar dokokin kasar zai jagoranci mabiyansa zuwa sakatariyar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin sanar masu da kudirinsa na shiga tseren kujerar shugabancin kasa a 2019.

2019: Tsohon gwamnan Plateau, Jonah Jang zai bayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa a yau
2019: Tsohon gwamnan Plateau, Jonah Jang zai bayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa a yau
Asali: Getty Images

Akalla yan siyasa 15 ne suka nuna ra’ayinsu na son takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 a karkashin lemar PDP.

Tuni dai sakatariyar PDP a jihar Plateau ta kammala shirye-shirye gabannin kaddamar da kudirin Jang a yau.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama wasu ma’aurata masu tabbin hankali dauke da sassan jikin dan Adam a Lagas

A baya Legit.ng ta rahoto cewa daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Kabiru Turaki, ya bayyana cewa jam’iyyar na bukatar daukar mutun mai martaba da mutunci a matsayin dan takarar shugaban kasa idan har tana so ta lashe zaben shugaban kasa a 2019.

Tsohon ministan na ayyuka na musamman da harkokin gwamnatin ya fadi hakan ne a Benin, jihar Edo yayinda yake jawabi ga tawaga da mambobin PDP kan kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Turaki yace shi ya cancanci kalubatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2019, inda ya kara da cewa kasar Najeriya na bukatar ba wai dan takara da ya san kan aiki ba kadai harda mai tarin ilimi kuma wanda baida bodadden hali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel