Shuwagabanni masu gaskiya ake bukata ba masu kwarin jiki ba - Attahiru Jega

Shuwagabanni masu gaskiya ake bukata ba masu kwarin jiki ba - Attahiru Jega

- Tsohon shugaban INEC ya bayyana ra'ayinsa game da irin kalar shugabannin da suka dace da kasar nan

- Wannnan na zuwa ne dai-dai lokacin da ake yada wani batu da ake alakanta shi ga shugaban kasar Amurka, na cewa shugaban Najeriya na a matsayin tamkar gawa ne

Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa kasar nan tana bukatar shuwagabanni masu gaskiya da rikon amana ba masu karfin jiki ba.

Attahiru Jega ya kara da cewa duk shugaban da ba shi da kwarewa tare da gaskiya to babu shakka komai kwarin jikinsa zai bige ne wajen lalata al'amura.

Shuwagabanni masu gaskiya ake bukata ba masu kwarin jiki ba - Attahiru Jega
Shuwagabanni masu gaskiya ake bukata ba masu kwarin jiki ba - Attahiru Jega
Asali: Depositphotos

Jegan ya bayyana hakan ne a wurin taron kungiyar lauyoyi ta kasa karo Na 58 wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja a jiya Litinin.

“Abin da muke bukata shi ne shugabanni masu adalci da kokarin tabbatar da aiyuka managarta wadanda aka tsara, sabo da haka ya zama wajibi mu tsaya mu nutsu domin ganin an samu shugabanni nagari ba kawai masu kwarin jiki ba" A cewar Jega.

KU KARANTA: Har yanzu muna fama da bashin N350bn da Kwankwaso ya bari – Gwamnatin Kano

Sannan ya kara da cewa “Talalabon shugaba zai iya ruguza al'amuran mulki haka shi ma shugaba mai kwarin jiki zai ruguza kowanne al'amarin cigaban kasa".

“Nagarta da gaskiya babban abin bukata ne a harkar shugabaci mai nagarta da adalci a tafarki irin na dimukuradiyya".

A nasa bangaren tsohon shugaban kasa Janar Abdusalami Abubakar mai ritaya, ya bayyana cewa zabubbuka a kasashen Afrika kullum suna karewa ne da rikice-rikice.

Ya kara da cewa ko da zaben kungiyar lauyoyi ta kasa sai da ya kare da cece-ku-ce.

“Tarihin rikicin siyasar Afrika na da nasaba da irin kafewar da shuwagabanni su ke yi domin ganin sun tabbata akan mulki. Suna bin hanyar dagewa wajen yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska. Wadannan shugabanni suna yiwa tsarin dimukuradiyya wani nakasu, musamman bangaren shari'a da zartarwa".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel