Na yi farin cikin jin muryan diyata – Mahaifin Leah Sharibu
- Yan kungiyar Boko Haram sun saki jawabin yarinya daya tilo da ta rage hannunsu
- Ta bukaci shugaba Buhari ya ceceta daga hannun miyagun
- Iyayenta sun tabbatar da cewa lallai muryarta aka saurara
Nathan Sharibu, mahaifin yarinya daya tilo dake hannun Boko Haram cikin yan matan da aka sace a makarantar Government Girls Secondary School, Dapchi, jihar Yobe, ya tabbatar da muryan da aka saurara ya fito daga Boko Haram.
A faifan rediyon, yarinyar wacce ke hannun yan Boko Haram tun watan Fabrairu ya kai kuka ga shugaba Muhammadu Buhari da ya tausaya mata.

An yi garkuwa da Leah Sharibu tare da kawayenta 118 amma yayinda aka sake sauran, Boko Haram sun cigaba da riketa saboda ta ki sauya addininta. Biyar daga cikinsu ne suka rasa rayukansu.
KU KARANTA: Ranar da Kwankwaso ya bar APC ban yi bacci ba don murna - Ganduje
Kungiyar daular addinin Musulunci a yammacin Afrika, wata balli daga kungiyar Boko Haram sun dau alhakin aikata satan yan matan.
Yayinda yake magana da jaridar Punch ranan Litinin, mahaifinta ya tabbatar da cewa lallai muryanta ne wanda aka saurara.
Yace: “Zan iya tabbatar da cewa muryar diyata Leah ne wannan. Ko shakka babu. Ina murnan jin muryanta,”
“Wannan ya kara min zaton cewa tana nan da rai. Kana kuma na yi farin cikin ganin sabuwar hotonta.”
“Bukatana daya da diyata. Gwamnati suyi na yi domin ceto ta”
Ya kara da cewa mahaifiyarta ta ji dadin jin muryarta amma za tafi jin dadi ranan da ta samu yanci.
Gabanin haka, mai magana da shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa hukumar DSS na duba faifan odiyon sannan ta dauki mataki bayan haka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng