Mummunar dabi’a: Yansanda sun kama yan luwadi guda 57 a jihar Legas

Mummunar dabi’a: Yansanda sun kama yan luwadi guda 57 a jihar Legas

Rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya, rundunar Yansandan jihar Legas ta sanar da kama yan luwadi guda hamsin da bakwai a yankin Egbede na jihar Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Kwamishinan Yansandan jihar, Edgal Imohimi ne ya bayyana haka ga manema labaru a ranar Litinin, 27 ga watan Agusta, inda yace Yansanda sun kama yan luwadin ne da misalin karfe biyu na daren Lahadi, a lokacin da ake kaddamar da sabbin yan kungiyar cikn harkar luwadi.

KU KARANTA: Toh fa! Hukumar Soji zata ladabtar da wasu Sojoji da suka tafka babban laifi a Maiduguri

“Mun samu bayanan sirri dake nuna cewa za’a kaddamar da wasu matasa cikin kungiyar yan luwadi da misalin karfe 1 zuwa 2 na daren Lahadi a dakin tara dake Otal din Kelly, wanda hakan ya saba ma sashi na 1 na dokar haramta auren jinsi.

“Da wannan ne muka aika da jami’an Yansanda a karkashin shugabancin CSP Oke Funmilayo da SP Solomon Fayemi zuwa wajen taron, inda suka hangi akalla matasa Tamanin, suna tsaka da shan haramtattun kwayoyi da kayan maye da suka hada da shisha, wiw, Tramadol.

“Sai dai a lokacin da suka hangi Yansanda, sai suka tarwatse, kowa ya ranta ana kare, amma jami’anmu sun samu nasarar damke mutane 57, zamu kaddamar da bincike akansu, kuma mu gurfanar dasu gaban Kotu da zarar mun kammala.” Inji Kwamishina Edgal.

Amma fa wasu daga cikin wadanda aka kama sun musanta zargin da Yansanda ke musu na yan luwadi, inda daga cikinsu mai suna James Obialu yace shi dan rawa ne, kuma ya halarci bikin ne don yin rawa aka kama shi.

Haka zalika wani mai suna Samuel Olarotimi yace akwai yan mata a wajen bikin, amma Yansanda basu kamasu ba, “Ban san dalilin daya hana Yansanda kama yan matan ba.” Inji shi, shi kuma Bob China yace ya rako abokinsa daya kawo abinci wajen bikin ne, yana waje aka kama shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel