Kwankwasiyya: Dubunnan mutane za su cika Abuja domin halartar shirin tsayawa takarar Kwankwaso

Kwankwasiyya: Dubunnan mutane za su cika Abuja domin halartar shirin tsayawa takarar Kwankwaso

Labari ya zo gare mu cewa ana tunani mutane fiye 150, 000 za su halarci bikin tsayawa takarar tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda za ayi a cikin tsakiyar makon nan.

Kwankwasiyya: Dubunnan mutane za su cika Abuja domin halartar shirin tsayawa takarar Kwankwaso
Kwankwaso zai tsaya takarar Shugaban kasa a Jam'iyyar PDP

Dama kun ji cewa Injiniya Rabiu Kwankwaso zai kaddamar da shirin tsayawa takarar Shugaban kasa karkashin babban Jam’iyyar adawa ta PDP a Ranar Laraba. Ana sa rai mutane da dama za su cika Garin Abuja makil a Ranar.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai yi wannan babban taro ne a farfajiyar Eagles Square da ke cikin babban Birnin Tarayya Abuja da kimanin karfe 10:00 na safe. Yanzu haka dai ana kammala shirye-shirye domin wannan taro.

Wani wanda yake cikin tafiyar Kwankwasiyya ya bayyanawa NAIJ Hausa cewa mutane da dama daga bangarorin kasar nan za su cika Birnin Tarayyar Abuja a Ranar Laraba. Ko da dai wasu sun ce ya fi dacewa ayi taron a Garin Kano.

KU KARANTA:

Wani Bawan Allah da yake cikin kwamitin gudunarwa na wannan taro da za ayi ya bayyana mana cewa ana kiyasata cewa Jama’a fiye da 150, 000 da kuma manyan mutane za su halarci wanann biki. Za kuma a kira Makada da Mawaka.

Kawo yanzu dai tsohon Gwamnan yana cigaba da ganawa da manyan PDP na Kasar domin ganin ya samu tikitin takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar. Sauran ‘Yan takarar dai sun hada da Atiku Abubakar da kuma irin su Ahmad Makarfi.

Dazu kun ji cewa Atiku ya jadaddawa sauran ‘Yan takarar PDP sai ya ga abin da ya turewa buzu nadi a wajen yakin neman kujerar Shugaban kasar. Atiku yace dole ya karasa ladan sa har ya samu yayi takara da Shugaba Buhari a zaben 2019

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel