Rundunar Ofireshon Lafiya Dole tayi rugu-rugu da mayakan kungiyar Boko Haram a Borno

Rundunar Ofireshon Lafiya Dole tayi rugu-rugu da mayakan kungiyar Boko Haram a Borno

A jiya, Lahadi, 26 ga watan Agusta, ne dakarun rundunar soji ta 82 dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno karkashin "Ofireshon Lafiya Dole, sun ragargaji wasu mayakan kungiyar Boko Haram a garin Kulamari dake karamar hukumar Kukawa.

Dakarun sojin ne suka tunkari 'yan kungiyar ta Boko Haram bayan samun labarin cewar suna garin Kulumari inda suke tilasta jama'a biyan haraji da kwace masu kayayyakin amfani na yau da kullum.

Rundunar Ofireshon Lafiya Dole tayi rugu-rugu da mayakan kungiyar Boko Haram a Borno
Rundunar Ofireshon Lafiya Dole tayi rugu-rugu da mayakan kungiyar Boko Haram a Borno

An samu musayar wuta tsakanin mayakan kungiyar da dakarun soji. Uku daga cikin 'yan Boko Haram din sun mutu yayin musayar wutar, kamar yadda Birgediya Janar Texas Chukwu, darektan hulda da jama'a na hukumar soji, ya sanar.

DUBA WANNAN: Kungiyar kablar Igbo (Ohanaeze) tayi kakkausar suka da gargadi ga gwamnatin Buhari

Daga cikin makaman da aka samu bayan ragargazar mayakan kungiyar ta Boko Haram akwai; bindigar samfurin AK47 guda uku, alburusai da kwanson su.

Sanarwar da Chukwu ya fitar ta kara da cewar dakarun soji sun cigaba da fatattakar mayakan kungiyar Boko Haram da suka gudu daga maboyar su bayan fuskantar ruwan wuta daga sojojin Najeriya.

Hukumar soji ta bukaci jama'a su sanar da ita duk wani al'amuran mutanen da basu yarda da su ba domin daukan matakin gaggawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng