Ga wuri-ga waina: PDP ta kalubalanci APC zuwa muhawarar keke-da-keke
- PDP ta takali hancin Shugaba Buhari
- Tace tana gayyatar sa muhawara
- Tace Shugaba Buhari ya gaza
Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya tace tana kalubalantar jam'iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa ga wata muhawara ta keke-da-keke.
Jam'iyyar ta PDP haka zalika ta ce manufar yin hakan shine domin su tattauna akan al'amurran da suka shafi yau da kullum da kuma harkokin mulkin kasar ta yadda al'umma masu zabe za su tantance inda aka dosa.

KU KARANTA: Labarin wani kare mai zuwa masallaci sau 5 a Zariya
Legit.ng ta samu cewa wannan kiran dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da mai magana da yawun jam'iyyar kuma babban sakataren yada labaran ta Mista Kola Ologbondiyan ya fitar ya kuma rabawa manema labarai.
A wani labarin kuma, mun samu cewa daya daga cikin 'yan majalisar dattawan a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a Najeriya dake wakiltar jihar Ogun shiyyar gabas watau Sanata Buruji Kashamu na shirin komawa jam'iyya mai mulki ta APC.
Wannan dai kamar yadda muka samu labari yana da nasaba ne da korar sa da jam'iyyar ta PDP tayi sakamakon laifuffukan da ya tafka a cikin jam'iyyar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng