Naira dubu 100: Wata kabila a Arewa ta takaita kudin sadaki da bidi'o'in aure

Naira dubu 100: Wata kabila a Arewa ta takaita kudin sadaki da bidi'o'in aure

- Kabilar Tiv ta kayyade kudin da samari za su kashe wajen aure

- Sun ce ba wanda zai kara kashe sama da Naira dubu 100

- Samari da 'yan mata na ta murna

Majalisar dattawan kabilar Tiv dake a jihar Benue ta Arewa ta tsakiyar Najeriya watau Tiv Area Traditional Council (TATC) a turance ta yanke hukuncin soke dukkan wasu kagaggun bidi'o'in da ake yi a yayin aure tsakanin 'ya'yan kabilar.

Naira dubu 100: Wata kabila a Arewa ta takaita kudin sadaki da bidi'o'in aure
Naira dubu 100: Wata kabila a Arewa ta takaita kudin sadaki da bidi'o'in aure

KU KARANTA: Labarin wani kare mai zuwa masallaci sau 5 a Zariya

Haka zalika majalisar dattawan ta kuma kayyade kudin sadaki da dukkan abun da ango zai kashe a lokacin auren a tsakanin masoya 'ya'yan kabilar da cewa ba zai wuce Naira dubu 100 ba.

Legit.ng ta samu cewa majalisar dattawan itace ta sanar da hakan a cikin wata sanarwar bayan taro da ta fitar a ranar Juma'ar da ta gabata a karkashin shugaban ta watau Farfesa James Ayatse.

Haka zalika majalisar kamar yadda muka samu, sun saka dokar cewa dukkan wadanda za su yi aure a tsakanin 'yan kabilar to lallai dole sai sun cika shekarun balaga na akalla shekaru 18 a duniya.

A wani labarin kuma yanzu haka dai harkokin tattalin arziki na cigaba da tabarbarewa yayin da baitul mali na Najeriya a babban bankin kasar watau Central Bank of Nigeria ya yi kasa da dalar Amurka miliyan 990 a cikin sati uku kacal da suka shude.

Wannan dai na kunshe ne a cikin rahoton da babban bankin ya fitar majiyar mu kuma ta Punch ta same shi a ranar Lahadin da ta gabata.

Tuni dai matasa suka nuna matukar jin dadin su game da wannan matakin na dattawan kabilar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel