‘Yan garin Atiku sun yi murna da titin da gwamnatin Buhari zata yi musu

‘Yan garin Atiku sun yi murna da titin da gwamnatin Buhari zata yi musu

- Wani aiki da gwamnatin tarayyana ta kaddamar ya sanya murmushi a fuskar mutanen mazabar Atiku Abubakar

- Titin dai ya shafe kimanin shekaru kusan 20 a lalace ba tare da gyara ba

A ranar Asabar din nan ne gwamnatin shugaba Muhammad Buhari ta kaddamar da fara aikin hanyar Mayo Belwa zuwa Jada ta wuce Ganye har Toungo, wanda bikin kaddamarwar ya jawo hankulan mazauna yankin da dama.

Da arziki a garin wasu: ‘Yan garinsu Atiku sun yi murna da titin da gwamnatin Buhari zata yi musu
Da arziki a garin wasu: ‘Yan garinsu Atiku sun yi murna da titin da gwamnatin Buhari zata yi musu

Wannan yankin shi ne mahaifar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman takarar shugabancin kasar nan, wato Atiku Abubakar wazirin Adamawa.

Tun da farko dai hukumar asusun amintattu na rarar man fetur wato PTF karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ne ya yiwa hanyar kwaskwarima, wanda kuma tun daga lokacin har gwamnatin Obasanjo ta yi shekarunta takwas, wanda kuma Atikun ne mataimakin shugaban kasa a lokacin amma ba su kula hanyar ba.

Al'umma da sauran masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun sha yin magana akan lalacewar hanyar, musamman ta yin la'akari da irin fitattun mutanen da suka fito daga yankin, wadanda su ka har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan rusasshshiyar jihar Gongola da tsohon shugaban jam’iyyar PDP wato Bamanga Tukur da kuma Ambadasa Hassan Tukur.

KU KARANTA: Bolaji Abdullahi ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar gwamnan Kwara

Wani mazaunin yankin mai suna Gambo Hardo ya bayyana cewa aikin hanyar zai yi tasiri sosai a zaben Shekarar 2019.

"Masu ruwa da tsaki na yankinmu ba su yi wannan aikin ba a lokacin da ludayinsu yake kan dawo, sai dai sun kwashe albarkatun aikin".

A nasa bangaren karamin ministan aiyuka, gidaje da makamshi Engr. Mustapha Shehuri

ya bayyana cewa aikin titin mai nisan kilomita 112 yana daga cikin alkawurran da jam’iyyar APC ta yi a lokacin da take yakin neman zabe.

"Aikin titin mai tsahon kilomita 112 wanda ya yi matukar lalacewa, babbar hanya ce da ta hada jihar Taraba da Jamhuriyar Kamaru, har zuwa gurin aikin wutar nan na Mambila".

"Sabo da amfanin wannan hanya ya sanya shugaba Muhammad Buhari ya jajirce wajen ganin an fara aikin, musamman idan aka yi la'akari da irin amfanin gonar da yake yankin, tare kuma da hada al'umma da gurin shakatawa na Gashaka Gumti".

A nasa bangaren shugaban sarakunan masarautar Ganye wato Gangwari Ganye, Umaru Sanda ya godewa gwamnatin tarayya bisa wannan aikin hanyar da aka yi watsi da ita tsohon shekaru 20.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel