Labarin wani kare da ke zuwa masallaci Sallah sau 5 a rana a garin Zariya

Labarin wani kare da ke zuwa masallaci Sallah sau 5 a rana a garin Zariya

Wani batu da ya dade yana daurewa jama'ar unguwar Tudun Wada a garin Zariya kai da ma al'ummar musulmi da dama shine labarin wani kare da ke zuwa masallaci wajen Sallah sau biyar a kullum rana tare da musulman unguwar.

Da majiyar mu ta zanta da mai karen, Jubril Mohammed, ya shaida mata cewa babu mai jan karen zuwa masallaci shine ke kai kan sa da zarar ya ji kiran sallah kuma da an kammala ya taso ya taho gida ya jira kiran sallah na gaba kuma.

Labarin wani kare da ke zuwa masallaci Sallah sau 5 a rana a garin Zariya
Labarin wani kare da ke zuwa masallaci Sallah sau 5 a rana a garin Zariya

KU KARANTA: Wani gwamnan APC ya sha ihu a wajen taro

Legit.ng ta samu cewa Malam Jubril ya kara da bayyana cewa karen ya soma yin hakan ne kusan shekaru bity da suka gabata kuma ma yanzu har zuwa jana'iza yake yi kuma a duk inda yaje, yakan samu wuri ne kusa da jama'a ya zauna har su kammala.

Da aka tambayi masana kimiyyar dabbobi ko me za su ce game da hakan, sun bayyana cewa daman akwai dabbobin da Allah yayi wa baiwar kwaikwayon mutane tare da dabi'antuwa da wata halayya idan har an koya masu wanda kare ma yana ciki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel