Zamu kawo hari: 'Yan bindiga sun aikawa garuruwa 4 sako a Arewa

Zamu kawo hari: 'Yan bindiga sun aikawa garuruwa 4 sako a Arewa

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun aika da sakon ban tsoro da razanarwa ga al'ummar garuruwa hudu a karamar hukumar Rabah ta jiha Sokoto dake da iyaka da jihar Zamfara inda suka sanar da su zuwan su a cikin 'yan kwanakin nan.

Majiyar mu ta Daily Nigerian dai ta bayyana cewa garuruwan da 'yan bindigar suka aikawa sakon sun hada da Ruwan Tsamiya da Kursa da Kaiwar Dawa da kuma Malela duk dai a karamar hukumar ta Raba.

Zamu kawo hari: 'Yan bindiga sun aikawa garuruwa 4 sako a Arewa
Zamu kawo hari: 'Yan bindiga sun aikawa garuruwa 4 sako a Arewa

KU KARANTA: Ibtila'i ya afkawa yan shi'a a Iran

Legit.ng ta samu cewa 'yan bindigar sun kuma bukaci 'yan garuruwan da su tara masu makudan kudade idan dai har ba su so su rirar masu.

A wani labarin kuma, Adadin danyen bakin man da kasar Amurka ke saye daga kasar Najeriya da ke a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a yanzu haka yayi kasa da ganga miliyan uku a duk wata adadin da bai taba kai hakan ba a duk 'yan kwanakin nan.

Wannan dai kamar yadda masana tattalin arzikin kasa suka yi fashin baki ba abu bane da zai haifarwa da kasar da mai ido musamman ma yanzu da tattalin arzikin kasar ke farfadowa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel