Munsha azaba a hannun DSS tsawon shekaru biyu -Clinton

Munsha azaba a hannun DSS tsawon shekaru biyu -Clinton

- Matasa bakwai yan kabilar Ijaw da ke tsare sun samu yancin komawa Bayelsa.

- Sun bayyana cewa tsawon shekaru biyu suke shan azaba a kurkukun dake karkashin kasa.

- A makwanni biyu da suka gabata ne sabon shugaban hukumar DSS ya ce zai waiwayi wadanda ake tsare dasu ba bisa ka'ida ba.

Za'a iya cewa sabon shugaban hukumar tsaro ta fararen kaya DSS, ya fara cika alkawuran da ya dauka a lokacin kama aiki, na cewa zai wai wayi wadanda hukumar ke tsare dasu, don sanin hukuncin da za'a dauka akansu. Ko dai sallama, ko kuma zuwa Kotu.

Bayanan da Legit.ng Hausa ta tattara a jiya, ya tabbatar da cewa, wasu matasa bakwai yan kabilar Ijaw dake jihar Bayelsa, sun samu yanci bayan shafe shekaru biyu a hannun jami'an DSS.

A makwanni biyu da suka gabata ne, Legit.ng ta ruwaito cewa sabon shugaban riko na hukumar, Mr, Mathew Seiyefe, ya yi alkawarin duba matsayar wadanda hukumar ke tsare da su, da zummar sallamar wadanda ake tsare da su ba bisa ka'ida ba.

An kawo matasan bakwai daga shelkwatar hukumar DSS da ke Abuja zuwa garinsu Yenagoa a karshen satinnan, in da aka sallame su a gaban yan uwansu da suka taru wajen ofishin hukumar na jihar.

Da yawa daga cikin wadanda aka sallama, sun fashe da kuka, tare da rungumar yan uwansu cikin murnar samun yanci. Da yawansu babu alamar kulawar tsafta a tattare da su.

KARANTA WANNAN: Wani Mutum ya kashe kansa bayan ya sha Tabar Wiwi ta yi ma sa karo

Daya daga cikinsu mai suna Clinton Ohaigbofa, ya ce sun baro ana ta sallamar wadanda ake tsare da su ba bisa ka'ida ba. A cewar sa, an kulle su a wani kurkuku da ke karkashin kasa a Abuja, wanda suke shan azaba a kowace rana.

Da ya ke bada labarin yadda ta faru har suka shiga komar hukumar ta DSS, ya ce "Babu abinda mukayi. An kamamu ne a ranar 24 ga watan Mayu, 2016. An kaimu shelkwatar jami'an tsaro ta JTF da ke Opolo, daga bisani aka wuce damu DMI da ke Abuja.

"Bayan sun tuhumemu, sai aka mayar damu wajen hukumar tsaro ta musamman DIA, a ranar 26 ga watan Augusta, 2016. A nan ne kuma suka dauke mu zuwa wajen hukumar tsaro ta fararen kaya, inda aka kullemu tsawon shekaru biyu"

Dangane da irin rayuwar da sukayi a cikin kurkukun DSS, ya ce "Sun gana mana azaba sosai, sun kullemu a wani kurkuku da ke karkashin kasa. Sukan bamu biredi dan kadan da safe, shinkafa yar kadan da rana, da kuma cikon hannun tuwo da daddare."

"Wannan abinci da suke bamu, ba zai isa ya kosar da jariri dan shekaru biyu da haihuwa ba. Abun bakin cikin shine, ko sau daya ba su kaimu kotu ba, sun tauye mana duk wani yanci namu. Bamu da yancin ganin ko da hasken rana, kullum cikin azaba muke.

"Sun barmu mun galabaita saboda yunwa, uwa uba sun hanamu ganin koda likitan da zai duba lalurorin dake damunmu. Amma a yanzu, ana ta sallamar wadanda ake tsare da su, tunda sabon shugaban hukumar ya kama aiki. Ba zan iya sanin adadin wadanda aka sallama ba, amma dai muna godiya ga sabon shugaban hukumar DSS"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel