2019: Jam'iyyar APGA ta damka takarar shugaban kasa ga dan arewa

2019: Jam'iyyar APGA ta damka takarar shugaban kasa ga dan arewa

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, kwamitin amintattu na jam'iyyar APA ya bayyana cewar dan takarar su na shugaban kasa zai fito daga arewacin Najeriya ne.

Bayan tashi daga wani taro na shugabannin jam'iyyar a Awka, babban birnin jihar Anambra, jam'iyyar ta bayyana cewar ta mika kujerar takarar shugaban kasa ga yankin arewa sannan dan takarar mataimakin shugaban kasa zai fito daga yankin kudu maso gabas.

A takardar sanarwa da jam'iyyar ta fitar, ta sanar da cewar ta gudanar da taron ne a fadar gwamnatin Anambra a matsayin karramawa ga jagoran APGA na kasa, gwamna Willie Obiano.

2019: Jam'iyyar APGA ta damka takarar shugaban kasa ga dan arewa
Dan takarar Jam'iyyar APGA a zaben 2015, Labaran Maku

Sanarwar ta bayyana cewar jam'iyyar APGA ta tattauna muhimman batu da suka shafi makomar ta da kuma lamuran da suka shafi siyasar Najeriya, musamman zaben shekarar 2019 mai zuwa.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya bayyana dalilin da ya saka shi yin tattakin mita 800 ranar Sallah

Da yake karin bayani ga manema labarai a garin na Awka, sakataren kwamitin amintattu na APGA, Alhaji Sani Shinkafi, ya bayyana cewar jam'iyyar zata samar da dan takara daga arewa da zai warware matsalolin Najeriya idan ya ci zabe.

Da yake amsa tambaya a kan mutumin da jam'iyyar zata tsayar takara, Shinkafi, ya ce tabbas akwai babban dan siyasa daga arewa da APGA zata tsayar. Sai dai bai ambaci suna ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel