Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi yayin gudanar da bikin sallar sa a Daura

Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi yayin gudanar da bikin sallar sa a Daura

- Buhari ya kammala hutun sa na Sallah

- Yau da marece ya koma fadar sa a garin Abuja

- Tun ranar Litinin yana gidan sa a Daura

Ba da dadewa bane dai Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bar mahaifar sa ta garin Daura, a cikin jihar Katasina zuwa fadar mulkin sa dake a garin Abuja, babban birnin tarayya Abuja.

Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi yayin gudanar da bikin sallar sa a Daura
Abubuwa 5 da shugaba Buhari yayi yayin gudanar da bikin sallar sa a Daura

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun samu nasarar kan yan Boko Haram

Shugaba Buhari dai ya shafe akalla kwana shida a garin na Daura inda yaje domin gudanar da bukukuwan sallah babba tare da 'yan uwa da kuma dangin sa.

Legit.ng ta tattaro mana wasu muhimman abubuwan da suka dauki hankalin jama'a da ya gudanar a lokacin zuwan nasa:

1. Yayi tattaki a kafa daga Sallar Idi zuwa gidan sa.

Wannan batun ya jawo ce-ce-ku-ce bayan da fadar shugaban Najeriya ta ce tafiyar da ya yi din a kasa ta tsawon mita 800 ta nuna cewa a shirye yake a ci gaba da shugabancin kasar

2. Shugaba Buhari ya gana da masu yiwa kasa hidima dake a garin na Daura inda daga baya ma har yayi masu sha tara ta arziki.

3. Shugaba Buhari din ya kuma gana da gwamnoni da kuma 'yan majalisu karkashin jama'iyyar sa ta APC da suka je masa ziyarar barka da sallah.

4. Kamar yadda ya saba kuma, Shugaba Buharin ya gana da wasu abokan sa 'yan ajinsu a makarantar firamare.

5. Shugabannin kungiyar 'yan kasuwar jihar Kano da ma mambobin kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Katsina suka kai wa Shugaba Buhari ziyara suma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel