Labarin Emmanuel Nwude - wani dan damfarar da ba'a taba irin sa ba a tarihin Najeriya

Labarin Emmanuel Nwude - wani dan damfarar da ba'a taba irin sa ba a tarihin Najeriya

- Emmanuel Nwude ya kure tsantsar iskanci

- Shi filin jirgin Najeriya ma taba saidawa

- Lamarin ya faru a shekarar 1995 zuwa 1998

Duk da dai kasar Najeriya na fama da wasu irin matsalolin da ita kadai ke da su, kamar sauran kasashe kasar na da hazikai a dai dai lokacin da kuma take da hatsabibai da daman gaske.

Labarin Emmanuel Nwude - wani dan damfarar da ba'a taba irin sa ba a tarihin Najeriya
Labarin Emmanuel Nwude - wani dan damfarar da ba'a taba irin sa ba a tarihin Najeriya

Labarin Emmanuel Nwude - wani dan damfarar da ba'a taba irin sa ba a tarihin Najeriya
Labarin Emmanuel Nwude - wani dan damfarar da ba'a taba irin sa ba a tarihin Najeriya

KU KARANTA: Masana kimiyya sun gano abun mamaki a duniyar wata

A yau dai muna dauke ne da labarin wani mutum dan Najeriya daga kudancin kasar nan mai suna Emmanuel Nwude da ya taba tafka damfarar da ba'a taba yin irin ta ba kuma har yanzu al'umma ke mamakin ta.

Legit.ng ta samu cewa Emmanuel Nwude ya taba damfarar wani mashahurin mai kudi ne dan kasar Burazil mai suna Nelson Sakaguchi inda ya saida masa filin jirgin da babu shi kwata-kwata akan makudan kudaden da suka kai dalar Amurka 242 a tsakanin shekarar 1995 zuwa 1998.

Kamar yadda muka samu, Emmanuel Nwude babban Darakta ne a bankin UBA a lokacin wanda kuma a nan ne ya samu damar damfarar mai kudin na kasar Burazil inda yayi shigar burtu a matsayin shugaban babban bankin Najeriya watau CBN.

Kamar dai yadda muka samu, ya cema mai kudin ne akwai wani filin jirgi da gwamnatin Najeriya zata saida kuma idan har ya siya to zai ci riba mai tsoka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel