Da duminsa: Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar Ofireshon Daji, Diran Mikiya

Da duminsa: Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar Ofireshon Daji, Diran Mikiya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar dakarun soji ta "Ofireshon Sharan Daji, Dirar Mikiya" a jihar Zamfara

- Buhari ya kai ziyarar ne kafin ya bar garin Katsina inda jirginsa ke ajiye a filin tashi da saukar jirage na Umaru Musa Yar'adua tun bayan zuwansa Daura hutun Babbar Sallah

- A yau ne shugaba Buhari ya bar mahaifar sa, Daura, domin komawa Abuja

A yau, Asabar, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar dakarun soji ta "Ofireshon Sharan Daji, Dirar Mikiya" dake aikin da 'yan ta'addar da suka hana jihar Zamfara zama lafiya.

Buhari ya kai ziyarar ne kafin ya bar garin Katsina inda jirginsa ke ajiye a filin tashi da saukar jirage na Umaru Musa Yar'adua tun bayan zuwansa Daura hutun Babbar Sallah.

Da duminsa: Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar Ofireshon Daji, Diran Mikiya
Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar Ofireshon Daji, Diran Mikiya

Da duminsa: Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar Ofireshon Daji, Diran Mikiya
Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar Ofireshon Daji, Diran Mikiya

Shugaba Buhari ya yabawa dakarun sojin bisa sadaukarwa da kuma jazircewar su wajen yaki da aiyukan ta'addanci a jihar ta Zamfara.

Kazalika shugaba Buhari ya basu kyautar manyan shanu biyar domin kyautatawa ga dakarun sojin da suka yi bikin Sallah a dazukan jihar Zamfara.

Buhari ya kai ziyarar ta bazata ne domin nuna jin dadi da mika godiya ga dakarun sojin bisa nasarar da suke samu a yakin da suke yi da aiyukan ta'addanci a jihar.

DUBA WANNAN:

"Na zo nan ne domin domin yi maku godiya tare da nuna jin dadi na bisa irin kwazo da kokarinku a aikin da kuke yi na kakkabe 'yan ta'adda da suka addabi sassan jihar Zamfara.

"Kada ku manta cewar 'yan Najeriya sun zuba mana idanu domin tsaron rayukansu da dukiyoyinsu. Na gamsu matuka da yadda ku ke gudanar da aiyukan ku kuma ina mai kara yin kira gare ku da kada nuna wa 'yan ta'adda tausayi ko imani," a kalaman shugaba Buhari.

Da duminsa: Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar Ofireshon Daji, Diran Mikiya
Buhari ya kai ziyarar bazata ga rundunar Ofireshon Daji, Diran Mikiya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel