Yarinyar da ta bace a Legas ta bayyana a jihar Benin

Yarinyar da ta bace a Legas ta bayyana a jihar Benin

Hukumar 'yan sanda sun gano wata karamar yarinya da ta bace a yayin da ta tafi coci tare da iyayenta da mai kula da ita. Bayan an kwashe kwanaki ana cigiyar ta, 'yan sanda sun gano ta a jihar Edo.

Iyayen karamar yarinyar nan mai suna Elo Ogidi sun cika da murna da farin ciki a ranar Juma'a bayan an gano ta a wani gidan marayu da ke Benin a jihar Edo.

Rahottani sun bayyana cewa an sace Elo ne a Cocin Christ Embassy da ke Ikeja a Legas lokacin da iyayenta suka tafi da ita cocin a ranar 8 ga watan Yulin 2018.

Yarinyar da ta bace a Legas ta bayyana a jihar Benin
Yarinyar da ta bace a Legas ta bayyana a jihar Benin

A yayin da yake tabbatarwa manema labarai cewa an gano Elo, mahaifinta Okpogene Ogidi, ya shaidawa Punch a ranar Juma'a cewa an kuma kama wasu da ake zargin su suka sace ta.

DUBA WANNAN: An dakatar da DPO na 'yan sanda da ya kai samame a masallaci

Elo tana tare da mai kulawa da ita ne amma bayan ta tafi karabar cake da ake rabo sai ta dawo ta tarar da cewa Elo ba kujarar da ta barta a zaune.

An shigar da kara a caji ofis na Alausa kuma daga baya aka mayar da case din sashin masu binciken garkuwa da mutane a SCIID da ke Yaba a Legas.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa 'yan sanda sun gano yarinyar a ranar Juma'a ne kuma sun kama wasu mutane da ake zargin sune suka sace ta daga Legas.

Mahaifinta wanda ya yi hira da Punch a wayan tarho ya ce har yanzu hukumar 'yan sanda basu gama yi masa cikaken bayanin yadda diyarsa ta tsinci kanta a Benin ba.

Ya ce, "An gano ta a Benin. Zamu tafi ofishin 'yan sanda da ke Edo mu karbe ta. An fada min cewa an tsinto ta a gidan marayu bayan munyi cigiya a kafafen yada labarai wani ya gane ta kuma ya tuntube ni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel