Jihohi biyar da su kafi zaman lafiya a Najeriya

Jihohi biyar da su kafi zaman lafiya a Najeriya

Zaman lafiya na daya daga cikin ababen da ake la'akari dasu wajen lissafa nasarorin da cigaba a gwamnatance.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi alkawarin kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram amma kuma gashi yanzu rikicin makiyaya da manoma ya kunno kai duk da cewa an samu nasarori wajen yaki da ta'addancin.

Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya kwashe shekaru da dama yana fama da masu tayar da kayan baya na yankin Neja Delta.

Jihohin biyar da su kafi zaman lafiya a Najeriya
Jihohin biyar da su kafi zaman lafiya a Najeriya

A yau, Legit.ng binciko muku jihohi 5 mafi zaman lafiya a Najeriya, idan mai karatu ne neman jihohin mafi karancin rikicin kabilanci, siyasa ko addini sai ya cigaba da karantawa.

1. Babban birnin tarayya Abuja

Abuja ce cibiyar siyasar Najeriya kuma mafi yawancin manyan 'yan siyasan kasar suna da gidaje a Abuja hakan yasa akwai tsaro sosai. Tun shekarar 2014 da bam ya fashe a garin Abuja, ba'a sake samun wani babban harin ta'adanci ba har yanzu.

Jihohin da ke makwabtaka da Abuja na fama da rikicin makiyaya amma jami'an tsaro ba su bari rikicin ya shiga Abuja ba. Tabbas, Abuja na daya daga cikin gagaruwan masu zaman lafiya a Najeriya.

2. Jihar Kebbi

Jihar Kebbi na daya daga cikin jihohi masu zaman lafiya saboda babu rikicin siyasa ko addinin ko kabilanci a jihar.

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya taba cewa jihar Kebbi ce jiha mafi zaman lafiya a tarihin Najeriya. Wannan sheda na da ke tabbatar da cewa akwai zaman lafiya a Kebbi.

3. Jihar Sakkwato

Jihar Sakkwato na yankin Arewa maso yammacin Najeriya ne. Kusan dukkan jihohon da ke makwabtaka da Sakkwato na fama da matsalolin tsaro amma rikicin bai shiga jihar Sakkwato ba.

Babu 'yan ta'adda a jihar, babu rikicin makiyaya da manoma kuma Boko Haram ba su kai hari jihar ba. Duk da cewa akan samu fashi da makami jefi-jefi, jihar Sakkwato na cikin jihohi masu zaman lafiya.

4. Jihar Akwa Ibom

Kamar yadda tarihi ya nuna, babu rikicin addini a jihar Akwa Ibom. Galibin mutanen jihar mabiya addinin Kirista ne kuma suna zaune lafiya da juna.

Jama'ar Akwa Ibom suna haba-haba da baki daga kowanne kabila. Sauran kabilun Najeriya masu yawa suna zaune lafiya a jihar ba tare da fuskantar tsangwama ba.

A lokacin da matasan kudu ke tayar da kayan bayan, Akwa Ibom na cikin jihohin da masu tada kayar bayan basu da yawa.

5. Jihar Ebonyi

Jihar Ebonyi na daya daga cikin jihohin masu zaman lafiya duba da yada akwai karancin ayyukan laifi kamar tashin bam, fadar kungiyoyin asiri, rikicin addini da masu tayar da kayan baya.

A kudancin Najeriya, an san jama'a Ebonyi da haba-hab da baki kuma suna zaune lafiya da sauran kabilu da mabiya addinan da ke jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel