Najeriya za ta karɓi baƙuncin Shugabar 'Kasar Jamus, Merkel a ranar Juma'a

Najeriya za ta karɓi baƙuncin Shugabar 'Kasar Jamus, Merkel a ranar Juma'a

Mun samu cewa shugabar kasar Jamus, Angela Merkel, a ranar Larabar mako mai gabatowa za ta karade wasu kasashe uku dake nahiyyar Afirka inda z at ziyarci kasar Senegal, Ghana da kuma Najeriya.

Angela za ta shafe tun daga ranar Laraba zuwa Juma'a cikin kasashen uku tare da tawagarta ta tattalin arziki kamar yadda kakakin fadar gwamnatin ta, Ulrike Demmer ya bayyana cikin birnin Berlin a ranar Juma'ar da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, ana sa ran Merkel za ta gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a safiyar ranar Juma'a ta mako mai gabatowa a fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.

Najeriya za ta karɓi baƙuncin Shugabar 'Kasar Jamus, Merkel a ranar Juma'a
Najeriya za ta karɓi baƙuncin Shugabar 'Kasar Jamus, Merkel a ranar Juma'a

Legit.ng ta fahimci cewa, Shugaban kasar za ta fara ganawa da shugaban kasar Senegal, Macky Sall a ranar Laraba inda za su tattauna kan al'amurran da suka shafi habakar tattalin arziki na kasar.

Kazalika Angela za ta gana da shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, a babban birnin kasar na Acca a ranar Alhamis inda za su tattauna kan al'amurran tattalin arziki da kuma tsare-tsaren kasashen ketare.

KARANTA KUMA: Yadda ganawa ta da Shugaba Buhari ta kasance a garin Daura - Shehu Sani

Daga karshe Shugabar ta Jamus za ta kama hanyar Najeriya a ranar Juma'a inda za ta gana da shugaban kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, Jean-Claude Brou.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, shugaba Buhari zai gana da Angela a wannan rana ta Juma'a inda za su tattauna al'amurran da suka shafi ta'addanci da kuma matsalolin tururuwar yawan bakin haure zuwa nahiyyar Turai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel