Yadda wasu yan bindiga dadi guda 2 suka gamu da ajalinsu a jihar Kaduna

Yadda wasu yan bindiga dadi guda 2 suka gamu da ajalinsu a jihar Kaduna

Rundunar Yansandan jihar Kaduna ta sanar da kashe wasu gagga gaggan yan bindiga dake fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane a kauyen Sabon Birni dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a ranar 16 ga watan Agusta.

Legit.ng ta ruwaito mukaddashin kwamishinan Yansandan jihar, Ahmad Kwantagora ne ya sanar da haka, inda yace tun bayan bindige yan bindigan da Yansanda suka yi, hukumar ta baza komarta don farautar duk wasu masu aikata muggan laifuka dake jihar.

KU KARANTA: Girma ya fadi: Kotu ta daure wani Fasto shekaru 5 a Kurkuku kan satar kudi N984,450

“Dakarun Yansanda dake karkashin babban sufetan Yansanda tare da jami’an Operation Yaki sun diran ma wata mabuyar yan fashi da masu garkuwa da mutane a kauyen sabon birni, inda bayan wata doguwar musayar wuta, Yansanda suka raunata mutum biyu, wanda aka garzaya dasu asibitin Barau Dikko, a can aka tabbatar sun mutu.” Inji shi.

Kwamishinan yace sun gano bindiga guda daya kirar AK47 da alburusai da dama, sai dai yace bincike ya nuna yan bindigan ne suka kashe wani jami’in Dansanda mai suna Felix Yohanna a wani harin kwantan bauna a kauyen Jankasa.

Bugu da kari Kwamishinan yace sun kama wasu masu garkuwa da mutane su Takwas, yan fashi da makami guda takwas da yan damfara guda hudu da kuma wasu kananan barayi dake afka ma shagunan jama’a.

Daga karshe Kwantagora ya bayyana cewa rundunar zata cigaba da tabbatar da tsaro a jihar Kaduna, kuma zasu gurfanar da mutanen gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel