Gida bai koshi ba: Manyan ayyuka 69 Buhari ke malalawa a kudancin Najeriya

Gida bai koshi ba: Manyan ayyuka 69 Buhari ke malalawa a kudancin Najeriya

- Manyan ayyuka 69 Buhari ke malalawa a kudancin Najeriya

- Ministan yada labarai Lai Mohammed ne ya fadi haka

- Yace nan ba da dadewa ba zai lissafa su

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa akalla manyan ayyuka 69 ne take kan yi a yanzu haka a yankin kudu maso gabashin kasar nan.

Gida bai koshi ba: Manyan ayyuka 69 Buhari ke malalawa a kudancin Najeriya
Gida bai koshi ba: Manyan ayyuka 69 Buhari ke malalawa a kudancin Najeriya

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta gwalashe Kwankwaso

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kokarin karyata masu cewa shugaba Buhari bai yi wa yankin na kudu maso gabashin kasar nan komai ba tun bayan hawan sa.

Legit.ng ta samu cewa Lai Mohammed wanda yayi wannan bayanin a garin Ilori babban birnin jihar Kwara, ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa bane zai lissafa duka ayyukan a yankin domin kowa ya gani.

A wani labarin kuma, Yayin da zabukan gama-gari na shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, jama'ar kananan hukumomin Ukwa ta gabas da kuma ta Arewa dake a jihar Abia sun yi wa shugaba Buhari alkawarin ruwan kuri'un su a zabukan masu zuwa.

Majiyar mu ta ruwaito mana cewa al'ummar kananan hukumomin dai sun yi wannan alkawarin ne lokacin da tawagar wani masoyin shugaban kasar a jihar mai suna Ikechi Emenike ta kai masu ziyarar rangadi a karshen satin da ya gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel