Babu wata baraka a tsakanin mambobin APC a majalisar wakilai - Jibrin

Babu wata baraka a tsakanin mambobin APC a majalisar wakilai - Jibrin

Dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa an samu baraka tsakanin mambobin majalisar wakilai na jam'iyyar APC.

Honarabul Jibrin ya yi amfani da shafinsa na Twitter @AbdulAbmj inda ya ce babu kanshin gaskiya cikin rahoton da wasu kafafen yada labarai ke wallafawa na cewa kan 'yan majalisar ya rabu gida biyu.

Sai dai dan majalisar ya amince da cewa akwai wasu 'yan matsalolin cikin gida da suka taso tsakanin jiga-jigan mambobin jam'iyyar ta APC kana ya jadada goyon bayansa ga shugaban majalisa, Femi Gbajabiamila.

Babu wata baraka a tsakanin Sanatocin APC - Sanata Jibrin
Babu wata baraka a tsakanin Sanatocin APC - Sanata Jibrin

"Akasin rahotanin da ke yawa a kafafen yada labarai. Ina son in tabbatar da cewa babu rabuwar kawuna tsakanin shugabanin APC a majalisa. Akwai wata 'yar matsala da ta kunno kai kuma dama hakan yana faruwa. Zamu warware matsalar a tsakaninmu. Kan mu a hade yake kuma @femigbaja shine shugabanmu. Nagode," kamar yada ya wallafa a Twitter.

DUBA WANNAN: Yawan canja jam'iyya na da alaka da matsalar kwakwalwa - Tsohon gwamna Sylva

A baya, majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa kungiyar Parliamentary Support Group sun a karkashin jagorancin Sanata Jibrin sun cacaki shugabansu, Femi Gbajabiamila kan wata hira da ya yi da Premium Times.

A hirar da aka wallafa a ranar Talata, Mr Gbajabiamila ya ce kungiya daya ce kawai suke dashi a majalisar wakilai wanda hakan ke nuna yana kore wasu kungiyoyi masu goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari.

An gano cewa kalamansa ba su yiwa kungiyoyin magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari da di ba.

Bayan babban kungiyar jiga-jigan APC da Gbajabiamila ke jagoranta, akwai wasu kungiyoyi biyu da Honarabul Jibrin da kuma wani dan majalisa daga jihar Sakkwato, Musa Sarkin-Ada ke shugabanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel