Gwamnan Sokoto Tambuwal sam bai da hangen nesa – Yabo

Gwamnan Sokoto Tambuwal sam bai da hangen nesa – Yabo

Dazu mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wani babban ‘Dan siyasa a Jihar Sokoto yayi kaca-kaca da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal inda yace Gwamnan bai san inda ya sa kai ba.

Gwamnan Sokoto Tambuwal sam bai da hangen nesa – Yabo
Wani tsohon Kwamishina ya soki Gwamnatin Tambuwal

Alhaji Faruk Malami Yabo wani tsohon Kwamishina a Jihar Sokoto yace abubuwan cigaban al’umma sun tsaya cak tun da Gwamna Aminu Tambuwal ya karbi mulki a 2015. Yabo yace Gwamnan bai da hangen nesa.

Kamar yadda mu ka samu labari, Faruk Malami Yabo wanda ya rike Kwamishinan kudi da kuma na kananan Hukumomi ya bayyana wannan ne lokacin da yayi hira da wasu ‘Yan jarida jiya Alhamis a cikin Garin Sokoto.

KU KARANTA: Shugaban Majalisa Dogara ya aikawa Sarkin Musulmi takarda

Yanzu haka dai Faruk Malami Yabo yana neman Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC mai mulkin kasar. Tsohon Kwamishinan ya soki shirin da Gwamnan yake yi na gabatar da kasafin Biliyan 200 a shekara mai zuwa.

Babban ‘Dan siyasar yace abin da Jihar Sokoto ta ke samu a shekara kaf ba ya wuce Naira Biliyan 70. Ana da tunani dai Tambuwal zai mikawa Majalisa kasafin sama da Naira Biliyan 200 wanda da wuya Jihar ta samu wannan kudi.

Kwanaki kun ji cewa ana tunani Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yana cikin masu kokarin karbe Gwamnati daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari don haka ne ma aka ce ya bar APC ya koma Jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel