Abin da ‘Yan Juventus su kayi mani lokacin ina Real ya sosa mani zuciya - Ronaldo

Abin da ‘Yan Juventus su kayi mani lokacin ina Real ya sosa mani zuciya - Ronaldo

Gwarzon ‘Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa tafin da Magoya bayan Juventus su ka yi masa a lokacin da ya zura kwallo a ragar su a kakar bara ce ta sa ya koma taka leda a Kungiyar.

Abin da ‘Yan Juventus su kayi mani lokacin ina Real ya sosa mani zuciya - Ronaldo
Cristiano Ronaldo ya bayyana dalilin sa na komawa Juventus

Watanni 3 da su ka wuce ne aka kara tsakanin Real Madrid da Juventus a Gasar Zakarun Nahiyar Turai inda Ronaldo ya zura kwallaye 2 a gidan Juventus. A cikin kwallayen na Ronaldo akwai wanda ya watse a saman iska.

Wannan kwallo da Ronaldo ya ci ta shahara har wajen abokan adawar sa inda Magoya bayan Juventus su ka tashi tsaye su na tafawa Gwarzon ‘Dan wasan na Duniya. Wannan abu dai ya ja hankalin Ronaldo kwarai da gaske.

KU KARANTA: Ana rikici tsakanin wasu manyan Taurarin Kannywood

Cristiano Ronaldo wanda ya bar Real Madrid a kakar bana ya dawo Juventus yake cewa Magoya bayan Kungiyar su ka sa ya zabi Kulob din. Bayan nan kuma ‘Dan kwallon mai shekaru 33 ya ji dadin yadda aka tarbe sa a Italiya.

Tsohon ‘Dan wasan Real Madrid din ya godewa hidimar da Mabiya bayan Juventus su kayi masa inda kuma ya sha alwashin saka masu da kwallaye a filin wasa. Tashin Ronaldo daga Sifen bayan shekaru 9 dai ya ba mutane mamaki.

Ana tsakiyar buga Gasar cin kofin Duniya ne aka ji kwatsam babban ‘Dan wasan Duniya Ronaldo zai bar Real Madrid. ‘Dan wasan gaban da ake ji da shi ya tattara ya koma Juventus da taka leda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng