Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun cafke wasu hatsabibai masu kisan mutane a jihar Kano

Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun cafke wasu hatsabibai masu kisan mutane a jihar Kano

- Yan sanda sun samu nasarar cafke bata gari a Kano

- Snn cafke wasu masu kisan mutane da wasu masu kera bindigogi

- Jami'in hulda da jama'a na rundunar ne ya fadi haka

Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Kano sun sanar da samun nasarar cafke wasu mutane laifin kisan kaitare kuma da wasu biyu watau Rabiu Suleman da kuma Yahaya Abdulkadir da suka kware wajen kera muggan bindigu da sauran miyagun makamai a karamar hukumar Tudun Wada.

Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun cafke wasu hatsabibai masu kisan mutane a jihar Kano
Da dumin sa: 'Yan sandan Najeriya sun cafke wasu hatsabibai masu kisan mutane a jihar Kano

KU KARANTA: Kasashen duniya sun amince da tazarcen Buhari a 2019

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar Musa Magaji Majia ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a jihar.

Legit.ng ta samu cewa sanarwa ta zayyana cewa sun muggan makaman da suka hada da bindigu 11 da kuma harsasai 53 a hannun hatsabiban takadaran.

Yanzu dai sun ce suna bincike kan lamarin kuma da zarar sun kammala za su maka su kotu.

Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata a halin yanzu dake wakiltar jihar a majalisar dattijai, Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ya bayyana kalaman Gwamna Ganduje na cewar ba zai iya shiga Kano ba a matsayin abun dariya.

Sanata Kwankwaso ya yace gwamna Ganduje yaron dan siyasa ne da ba zai iya fitowa yayi siyasa da kafafun sa ba sai ya labe bayan Shugaba Buhari domin yasan bai da magoya baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel