Lafiya Jari: Masana sun zayyana illoli 4 da ke tattare da yin wanka kullum

Lafiya Jari: Masana sun zayyana illoli 4 da ke tattare da yin wanka kullum

- Masana sun gano illolin yin wanka kullum

- Sunce yana kawo bushewar fata

- Wanka sau biyu a sati ya isa

Tabbas Hausawa sunyi gaskiya da suka bayyana ilimi da kogi wanda ke da girman gaske ta yanda duk kokarin mutum ba zai iya debar sa duka ba sai dai ya dan kamfato inda yake kusa da shi.

Lafiya Jari: Masana sun zayyana illoli 4 da ke tattare da yin wanka kullum
Lafiya Jari: Masana sun zayyana illoli 4 da ke tattare da yin wanka kullum

KU KARANTA: Jahohin Najeriya 6 da suka fi yawan musulmai

To yanzun ma hakan ne ta kara tabbata bayan da wasu masana harkar kimiyyar lafiya dake a kasashen Amurka da Kanada dukkanin su a nahiyar Turai suka gudanar da wani bincike mai zurfi game da illolin dake tattare da yin wanka kullum.

Legit.ng ta samu cewa duk da dai masanan ba wai sun ce yin wanka na da illa ba ne ko kuma zama da dauda yana da kyau ba, amma dai sun bayyana cewa yin wankan koda sau daya ne kullum yana da matukar illa ga lafiyar dan adam.

Binciken dai ya gano cewa wanka sau daya ko biyu a sati ya ishi dan adam.

Masanan dai sun zayyana wasu matsalolin da suka gano kamar haka:

1. Yin wanka kullum kan iya jawo matsalar bushewar fata.

2. Yin wanka kullum kan jawo tsattsagewar fata.

3. Idan fata ta tsage kuwa, cututtuka da dama za su iya shiga jikin mutum.

4. Haka ma masu binciken sun ce yin wanka kullum kan wanke kwayoyin cuta masu anfani a jikin dan adam din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel