Mazajen mu basu gamsar damu yadda ya kamata - Inji matan jihar Kaduna

Mazajen mu basu gamsar damu yadda ya kamata - Inji matan jihar Kaduna

- Mazan mu basu gamsar damu da abinci mai gina jiki

- Da sun samu kudi aure suke karawa

- Lamarin na damun mu sosai

Matan aure dake a garim Gimba na karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna sun koka akan lamarin da suka ce yaki-ci-yaki-cinyewa na yadda mazajen su ke barin su da yunwa tare da rashin gamsar da su da abinci mai gina jiki.

Mazajen mu basu gamsar damu yadda ya kamata - Inji matan jihar Kaduna
Mazajen mu basu gamsar damu yadda ya kamata - Inji matan jihar Kaduna

KU KARANTA: Kasashen duniya sunce Buhari ya zarce a 2019

Matan dai sun bayyana hakan ne a yayin wani taron gama gari da wata kungiyar da ba ta gwamnati ba ta Save the Children International (SCI) ta shirya a garin domin gano musabbabin ciwalwatan yunwa da suka addabe su.

Legit.ng ta samu cewa matan da suka yi magana a wajen taron sun nuna rashin jin dadin su matuka game da yadda mazajen ke kula da su inda suka ce da sun samu kudi aure kawai suke karawa.

A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan Kano kuma Sanata a halin yanzu dake wakiltar jihar a majalisar dattijai, Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ya bayyana kalaman Gwamna Ganduje na cewar ba zai iya shiga Kano ba a matsayin abun dariya.

Sanata Kwankwaso ya yace gwamna Ganduje yaron dan siyasa ne da ba zai iya fitowa yayi siyasa da kafafun sa ba sai ya labe bayan Shugaba Buhari domin yasan bai da magoya baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel