Bafillace ya kashe abokinsa da suke kiwo tare a kan N2,000

Bafillace ya kashe abokinsa da suke kiwo tare a kan N2,000

A yau Alhamis ne wani Alkalin kotun majistare da ke zamanta a Iyaganku ya bayar da umurnin a daure wani makiyayi mai suna Jaye Mohammadu, da ya kashe abokinsa saboda N2000 a gidan yari dake Agodi.

Alkalin kotun, Mr Abdulateef Adesbisi, ya ce a bawa Muhammadu matsuguni a gidan yarin Agodi har zuwa lokacin da ofishin tuhumar masu laifi na jihar Oyo ta bayar da shawarar matakin da za'a dauka a kansa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ta ruwaito cewa kotu tayi watsi da rokon afuwa da lauyan Muhammadu, Mr Oritshuwa Uwawah, ya yi a lokacin da ya bayyana a kotu.

Bafillace ya kashe abokinsa da suke kiwo tare a kan N2,000
Bafillace ya kashe abokinsa da suke kiwo tare a kan N2,000

Alkalin kotun ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 25 ga watan Satumbar shekarar 2018.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Mutane 3 sun kone kurmus sakamakon wata mummunan hatsarin mota

Dan sanda mai shigar da kara, Cpl. Ojo Bewaji, ya shaidawa kotu cewa Mohamadu da marigayin, Gambo Tashi mai shekaru 22 duk suna yiwa wani Alhaji Kata dake Aba Olode na jihar Oyo kiwo ne.

Bewaji ya ce wanda ake tuhuma ne ya yi sanadiyar rasuwar abokin aikinsa ta hanyar sararsa da ya yi da adda a wuya.

Mai shigar da karar ya ce a ranar 30 ga watan Yulin wannan shekarar ne Muhammadu da Tashi suka koma gida bayan sun gama kiwo a ranar sai Muhammadu ya zargi Tashi da sace masa kudi N2,000.

"Zargin da ya yi masa ne ya haddasa rikici tsakaninsu har ta kai ga Muhammadu ya sari Tashi da adda a wuya yayin da Tashi ya ke rike da sandarsa ta kiwo."

Ya ce lamarin ya afku ne misalin a ranar 30 ga watan Yuli misalin karfe 12.35 na dare a Aba Olode, Kishi da ke jihar Oyo.

Acewarsa, laifin ya sabawa sashi na 316 da 319 na dokar masu aikata laifi na jihar Oyo na shekarar 2000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel