Buhari ya nemi ayi koyi da masu-gadin da su ka tsinci jakar wani mutumi su ka yi cigiya

Buhari ya nemi ayi koyi da masu-gadin da su ka tsinci jakar wani mutumi su ka yi cigiya

Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi mutane su yi koyi da wasu Bayin Allah 2 da ke gadi da su ka tsinci wata jaka cike da dukiya makil amma su ka nemi mai jakar su ka maida masu abin su.

Buhari ya nemi ayi koyi da masu-gadin da su ka tsinci jakar wani mutumi su ka yi cigiya
Wasu sun tsinci jaka da kudi a tashar jirgi sun nemi masu ita

Wannan abin mamaki ya faru ne a filin jirgin saman Najeriya ne Legas bayan da wani Likita ya jefar da jakar Matar sa a lokacin da ake sa kayan sa a cikin mota. Wadannan Bayin Allah dai sun ji tsoron Allah sun yi abin da ya kamata.

Shugaba Buhari ya ji dadin abin da wadannan mutane su ka aikata inda yace haka za a so a ga Najeriya ta koma. Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne ta bakin mai magana da yawun sa watau Mista Femi Adesina a cikin makon nan.

Banji Oyegbami wanda wani Likita ne a Legas ya bayyana yadda abin ya auku inda yace ya dawo daga Amurka ne sai ya jefar da jakar sa ba tare da kowa ya ankara ba, hakan dai duk bai hana wadannan mutanen su maido masa abin sa ba.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya sabawa Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo

Wannan abin ya faru ne a tashar jirgin sama na Murtala Muhammed inda masu gadin su ka kira masu jakar a waya cewa su dawo su dauki kayan su. A cikin jakar akwai daloli da agogo da wayoyin zamani da ba a dauki ko guda daga ciki ba.

Sunan wadannan masu gadi: Francis Emepueaku da Achi Daniel, kuma dai ko da aka yi kokarin ba su tukwuici ba su karba ba. Shugaban kasa Buhari ya yaba da gaskiyar wannan mutane wadanda su ka rike amana wanda tayi wuya yanzu,

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel