Muna bukatar Buhari ya sake kera tattalin aziki – Tinubu

Muna bukatar Buhari ya sake kera tattalin aziki – Tinubu

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, yace akwai bukatar Shugaban kasa mai jajircewa da mayar da hankali akan aiki kamar Muhammadu Buhari ya sake kera tattalin arzikin kasar.

Da yake Magana a lokacin bikin babban Sallah a Lagas, Tinubu yace: “Yan Najeriya na mulkin damokradiyya, zamu ci gaba da kasancewa a wannan gwamnati ta damokradiyya. Muna Bukatar Shugaba Buhari ya sake kera tattalin arziki, ma’ana abunda yake yi akan tattalin arziki yana yin shi a hankali, idan ba haka bama so mu sake faduwa.”

Muna bukatar Buhari ya sake kera tattalin aziki – Tinubu
Muna bukatar Buhari ya sake kera tattalin aziki – Tinubu

Tinubu yace yana alfahari da abunda yayi a jihar Lagas lokacin da yake a matsayin gwamna, cewa “mun jajirce mun mayar da hankali sannan mun daukaka ruhin mutanenmu kuma wannan shine muhimmin abunda yan Najeriya zasu mayar da hankali akai a yanzu.”

KU KARANTA KUMA: 2019: Yan Najeriya na son shugaban kasa mai gwaninta ne ba wai mai tafiya ba

Yace barayin gwamnati sun cinye baitul malin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel