Kwankwaso ya gana da su tsohon Shugaban kasa Jonathan

Kwankwaso ya gana da su tsohon Shugaban kasa Jonathan

Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da tsofaffin Shugabannin kasar Najeriya 2 a babban Birnin Tarayya Abuja a jiya a Ranar Larba da yamma.

Kwankwaso ya gana da su tsohon Shugaban kasa Jonathan
Kwankwaso ya sa labule da Janar Gowon Hoto daga: Saifullahi Hassan

Kamar yadda mu ka samu labari daga wani Hadimin Sanatan na Kano ta tsakiya, tsohon Gwamnan Jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a gidan sa da ke Maitama a cikin Abuja.

Bayan nan kuma Rabiu Kwankwaso wanda kwanan nan ya dawo daga Kudancin Najeriya inda yayi sallar idi, ya gana da tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon. Kwankwaso ya gana da Gowon ne a gidan sa da ke Asokoro a Abuja.

KU KARANTA: PDP ta nemi a yi maganin 'Yan Miyetti Allah a Najeriya

Kwankwaso ya gana da su tsohon Shugaban kasa Jonathan
Tsohon Gwamna Kwankwaso ya gana da Jonathan

Kafin nan dama dai tsohon Gwamnan yayi wani zama da Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta da kuma tsohon Gwamnan Jihar James Ibori. Ana tunani Sanatan yana neman goyon bayan manyan PDP ne a zaben fitar da gwani da za ayi.

Kwanaki kun ji labari cewa Shugaba Buhari yayi magana game da koshin lafiyar sa bayan sallar idi. Fadar Shugaban Kasa ta caccaki irin su Gwamna Aminu Tambuwal bayan Buhari yayi tattaki na kusan kilomita guda domin nuna koshin lafiyar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel