Jamiyyar PDP ta bukaci a kama shugabannin kungiyar Miyetti - Allah

Jamiyyar PDP ta bukaci a kama shugabannin kungiyar Miyetti - Allah

- Cikin yanayin abari ya huce, PDP ta mayarwa da kungiyar Fulani ta Miyatti Allah martani

- Babbar jam'iyyar adawar ta Najeriya ta bukaci hakan ne bayan da kungiyar ta yi wani kalami kan shugaban majalisar wakilai

Jamiyyar PDP ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya umarci jami'an tsaron kasar nan da su kame shugabannin kungiyar Miyetti Allah na kasa akan ikirarin da suka yi game da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, na cewa za su cire shi daga kan mukaminsa da karfin tuwo.

Jamiyyar PDP ta bukaci a kama shugabannin kungiyar Miyetti-Allah
Jamiyyar PDP ta bukaci a kama shugabannin kungiyar Miyetti-Allah

Jamiyyar ta kara da cewa wannan kadai ya isa manuniya akan irin shirin da jamiyyar APC take yi na ganin ta kawar da Bukola Saraki daga kan shugabancin majalisar dattawa ta kowanne hali.

Wannan kiran yana cikin wata sanarwa ne da kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya sanyawa hannu a yau laraba.

Ya kara da cewa kalaman da kungiyar ta Miyetti Allah ta yi ya bayyana cewa jam’iyyar APC tana da dangantaka da masu tayar da hankali, wanda hakan abu ne da zai kawo rabuwar kawunan al'ummar kasar nan.

KU KARANTA: Shugaban jam’iyyar APC na jihar Akwa-Ibom ya koma PDP

“Bisa wannan kalmomi na tayar da hankali gami da tarzoma da kungiyar Miyetti Allah ta yi, muke kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari da ya kame jagororin kungiyar cikin kasa da sa'o'i 24. Idan ba haka kuwa, babu shakka al'ummar kasar nan za su gaskata cewa lallai gwamnatin tarayya tana da hannun akan wadannan kalmomin da kungiyar Miyetti Allah ta yi." Ologbondiyan ya jaddada.

Kola ya cigaba da cewa “Wannan abu ne a zahiri da cewa masu tayar da tarzoma a jihohin Benue da Taraba da Zamfara da jihar Nasarawa da Plateau da Kaduna da Edo da Borno, da Yobe da kuma Enugu da jihar Kogi da Adamawa suna da masu daure musu gindi a cikin ‘yan siyasa, masu kokarin cimma bukatarsu wajen ganin an sauya shugabancin majalisar dattawa ta kowanne hali".

“Kafin kalmomin da kungiyar Miyetti Allah ta yi, mafi yawa daga cikin al'ummar kasar nan suna da masaniyar yadda kungiyar take wakiltar rundunar sojin kasar nan tare da shugaba Muhammad Buhari.

Amma sai ga shi abin takaici sun zama dirka ta hudu a tsarin dirakun mulkin kasar nan, wanda har suke ikirarin kawar da mutum na uku a tsarin shugabancin kasar nan daga kan mukaminsa".

Jamiyyar PDP na sane sarai cewa kungiyar Miyetti Allah bata wakilta tare da kare muradin da yawa daga cikin al'ummar Fulani ko wata kabila a fadin kasar nan." Kola Ologbondiyan ya shaida.

A karshe sanarwar ta bukaci al'ummar kasar nan masu kishinta da suyi Allah wadai da wannan kalmomin da kungiyar Miyetti Allah ta yi, wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel