Dabbobi 5,000 sarkin Saudiyya yayi layya da su bana (Kalli bidiyon)

Dabbobi 5,000 sarkin Saudiyya yayi layya da su bana (Kalli bidiyon)

- Sarkin Saudiyyya ya yi sadaka da dabbobin layya 5,000

- Raguna daya-daya aka rabawa mutanen da suka amfana

A kowani shekara, sarkin Saudiyya, Salman, kan dauki nauyin mahajjata da dama inda zai yi musu yankan layya. A bara, ya yanka dabbobi 2,400. Amma a shekaran nan, ya yanka dabbobi 5,000.

A bana, sarkin Saudiyya ya karbi bakuncin mutanen kasar Falasdinu da suka rasa iyalansu, yan kasar Sudan da annoba ya hallaka da kuma iyalan jami’an tsaron Misra da suka rasa rayukansu.

Sakataren shirin layyar, Abdullah bin Mudlaj ya bayyana cewa wannan abu da sarki keyi da karfafa zumuntar kasar Saudiyya da sauran kasashe daban-daban.

KU KARANTA: Ni gudun sama da mita 1609 nike yi, ba tafiyan mita 800 – Atiku ya yiwa Buhari Isgili

Game da cewar manyan jami’an kasar, Sarkin ya biya kudi dabbobi 5,000 kuma an sanar da wadanda hakan zai amfana. Wadanda suka samu wannan sadaka mutane 5000 ne daga kasashe 80.

Daya daga cikin masu amfana mai suna Ruwdha Abdulhameed, yar kasar Falasdin kuma mai shekara 63 da haihuwa ta rasa danta daya, da jikoki biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel