Tirelar Gas ta murkushe motar fasinjoji kamar Taliya amma ba wanda ya mutu

Tirelar Gas ta murkushe motar fasinjoji kamar Taliya amma ba wanda ya mutu

- Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana Muzuru ana Shaho sai yayi

- Wasu mutane sun tsallake rijiya da baya ana tsaka da bikin Sallah

A kalla wasu matafiya da ba su gaza 20 ba ne suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ake tsaka da bikin Sallah a garin Ore dake jihar Ogun, bayan da wata motar daukar Gas ta murtsike motar da su ke ciki.

Tirelar Gas ta murkushe motar fasinjoji kamar Taliya amma ba wanda ya mutu
Tirelar Gas ta murkushe motar fasinjoji kamar Taliya amma ba wanda ya mutu

Wani da abin ya faru akan idonsa ya ce matafiyan sun dan dakata ne a gefen hanya domin yin wani uzuri, mintuna biyar da ficewarsu daga cikin motar ta su al'amarin ya faru.

Rahotan da jaridar Vanguard ta rawaito ya bayyana cewa Tankar Gas din tana sharara gudun wuce sa'a ne, wanda hakan ya sanya direban motar ya kasa sarrafata, inda nan take ta afkawa motar fasinjojin dake ajiye a kofar gidan cin abinci da ke kan babbar hanyar Ore zuwa Lagos.

Ganin Faruwar wannan al'amarin ne ya sanya matafiyan murna tare da godewa Allah bisa tseratar da rayuwarsu da yayi daga wannan Ibtila'in.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya sallami Fursunoni 170 a jihar Kano

Babban baturen hukumar kiyaye haddura ta kasa Rotimi Adeleye ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Tankar Daukar Gas din ta afkawa wata mota mai cin mutane goma sha hudu dake tsaye a wani kofar gidan abinci na kan hanyar Ore zuwa Lagos" Adeleye Ya shaida.

“Sai da ta fara yin karo da wani sashe na wata gada kafin daga bisani ta afkawa motar fasinjojin. Babu asarar rayuka domin dukkanin matafiyan sun shiga wani gidan abinci suna cin abinci a lokacin da abin ya faru".

Jami’in ya tabbatar da cewa “Ba'a samu fashewar tankin da ke dauke da Gas din ba a lokacin da hatsarin ya faru"

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel